Shugabannin APC, Kwamishinoni, Sarakuna, sun tsure bayan an gano Akeredolu ya kamu da COVID-19
A ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2020, aka samu labari maras dadi cewa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN ya kamu da cutar COVID-19.
Shugabannin jam’yyar APC da ma’aikatan sakatariyar jam’iyyar sun kidime da samun labarin cewa Rotimi Akeredolu ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.
Rotimi Akeredolu ya halarci babban ofishin APC inda ya gabatar da takardun tsayawa takara, sannan kuma ya zanta da wasu jami’an jam’iyyar a birnin tarayya.
Jaridar This Day ta ce an ga gwamnan na jihar Ondo a wani bidiyo, ya na atishawa a sakatariyar.
Bugu da kari Akeredolu ya na cikin wadanda su ka halarci taron NEC da aka yi a ranar Alhamis a garin Abuja. Bayan nan ne aka ba gwamnan shawarar ya yi gwaji.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran manyan jam’iyyar APC sun halarci taron na NEC.
Bayan samun wannan labari, Yekini Nabena ya shaidawa jaridar This Day cewa za ayi wa duk wadanda su ke aiki a sakatariyar APC gwajin cutar COVID-19.
Jam’iyyar APC ta ce za ta bukaci jami’an hukumar NCDC su yi wa duk wanda ke ofishinta gwaji.
Kawo yanzu wasu manyan gwamnatin jihar Ondo da su ka hadu da Rotimi Akeredolu kafin a san cewa ya na dauke da wannan cuta sun samu kansu a cikin mummunan halin firgici.
KU KARANTA: Ina da COVDI-19 - Gwamna Rotimi Akeredolu
Jaridar Vanguard ta ce kwamishinoni da ‘yan majalisar dokoki da kuma sarakunan gargajiya da a makon da ya wuce su ka sada da gwamnan na jihar Ondo su na tsoron ace sun kamu da cutar.
A makon da ya wuce, kakakin majalisar jihar Ondo, Rt. Hon. Bamidele Oloyelogun ya jagoranci abokan aikinsa zuwa gaban mai girma Rotimi Akeredolu a ofishinsa a garin Akure.
Bamidele Oloyelogun da sauran ‘yan majalisar dokokin sun sayawa gwamnan fam din sake neman takara ne a ofishin jam’iyyar APC a babban birnin tarayya Abuja, su ka kawo masa har ofis.
Jaridar ta ce shugaban majalisar Sarakunan jihar Ondo, mai martaba Sarkin kasar Ugbo, Oba Frederick Akinruntan ya jagoranci takwarorinsa zuwa wajen gwamnan a makon da ya wuce.
Oba Frederick Akinruntan da sauran Sarakunan jihar Ondo sun je gidan gwamnati domin su yi wa gwamna Rotimi Akeredolu mubaya’a, su kuma jadadda goyon baya ga tazarcen da ya ke nema.
Bayan haka, mai girma gwamnan ya gana da kusan duka kwamishinoninsa a makon jiya. A halin yanzu gwamnan ya bukaci kwamishinonin na sa da su yi gwaji domin sanin halin da su ke ciki.
Akwai yiwuwar cewa gwamnan ya gogawa manyan jihar wannan cut aba tare da an sani ba.
Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Ondo, Donald Ojogo, ya fitar da jawabi, inda ya bayyana cewa hadimai da manyan mukarraban da su ka sadu da gwamnan za su yi gwaji.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng