Buhari: Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin ci gaba

Buhari: Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin ci gaba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kasar Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin ci gaba kuma tana bukatar a gyara alkiblar tattalin arzikinta, jaridar The Cable ta ruwaito.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 30 ga watan Yuni yayin da yayi taro da majalisar tattalin arziki ta kasa (PEAC).

"Muna cikin kasa ne mai yawan mutane matalauta, rashin isassun ababen more rayuwa, rashin gidaje da kuma tattalin arzikin da annobar korona ta yi wa illa tare da durkusar da kasuwan man fetur," yace.

Buhari: Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin ci gaba
Buhari: Najeriya na cikin mawuyacin halin rashin ci gaba Hoto: Reuters
Asali: UGC

A yayin gabatarwa, majalisar da ta samu jagorancin Doyin Salami, ta jinjina a kan yadda aka tabbatar da wasu daga cikin shawarwarinta.

Kamar yadda takardar da Garba Shehu yasa hannu ta bayyana, majalisar ta mika wasu tsauraran matakai da ya kamata a dauka don farfado da tattalin arziki.

Salami ya ce akwai babbar bukata a wurin shiryawa da kuma bayanai a tsakanin masana'antu, bangarori da cibiyoyin gwamnati.

Majalisar ta bada shawara a kan bada fifiko sannan a shirya aiwatar da manyan ayyuka tare da kammala su cikin watannin 12. A duba wadanda ba a kammala ba a kammala su cikin kankanin lokaci.

KU KARANTA KUMA: INEC ta yi barazanar dakatar da zaben gwamna a jihar Edo

Majalisar ta ce akwai bukatar gina gidaje tare da samar da ayyukan yi wadanda gwamnati da hukumomi masu zaman kansu za su dauki nauyi.

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban kasar ya gaggauta aminta da abinda majalisar tayi bayani a kai tare da sabbin shirye-shirye ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta ware wasu makudan kudade har naira biliyan 600 don tallafawa manoma da ke fadin kasar nan.

Ministan noma da raya karkara, Sabo Nanono ya sanar da hakan a yayin kaddamar da shirin manoma a jihar Kano.

Karin tabbacin hakan shine wallafar da hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi a shafinsa na sadarwa ta Twitter.

Ya ce an yi nufin mika kudin ga mutum 2.4 miliyan daga cikin manoman fadin kasar nan don daukar dawainiyar ayyukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel