Kano: Dakatattun 'yan majalisar dokokin jihar sun koma bakin aiki

Kano: Dakatattun 'yan majalisar dokokin jihar sun koma bakin aiki

- 'Yan majalisar dokokin Kano da aka dakatar sun koma bakin aiki a yau Talata, 30 a watan Yuni

- Sun jinjina wa banaren shari'a kan yadda ta tabbatar da adalcci wajen mayar dasu kujerunsu

- An dai dakatar da 'yan majalisar biyar ne saboda rashin da'a da kuma take dokokin majalisar yayin da ake kokarin tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Dakatattun 'yan majalisar jihar Kano a ranar Talata sun koma majalisar bayan hukuncin babbar kotun tarayya da ke jihar wacce ta bada umarnin mayar da su bakin aikinsu da gaggawa.

Daya daga cikin dakatattun 'yan majalisar, Bello Butubutu mai wakiltar mazabar Tofa da Rimin Gado, ya sanar da manema labarai cewa komawarsu majalisar shaida ce da ke bayyana rashin dogaro da kowa na ma'aikatar shari'a.

Butubutu, wanda ya yi magana a madadin sauran dakatattun 'yan majalisar, ya jinjinawa ma'aikatar shari'a a kan yadda ta bayyana cewa zaman kanta take da nuna adalci a kan dakatar da su da aka yi.

Kano: Dakatattun 'yan majalisar dokokin jihar sun koma bakin aiki
Kano: Dakatattun 'yan majalisar dokokin jihar sun koma bakin aiki Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Idan za mu tuna, a ranar 16 ga watan Mayun ne dakatattun 'yan majalisar suka tunkari kotu inda suke bukaci soke dakatarwar da aka yi musu tare da mayar da su bakin aikin su, bukatar da kotun ta aminta da ita.

Kamar yadda Butubutu ya ce, wannan al'amarin na nuna cewa ma'aikatar shari'a na yin iyakar kokarinta wurin ganin adalci ya tabbata, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

"Mun yi jinjina ga shugabannin majalisar jihar da suka karbi umarnin kotun tare da barinmu zaman majalisar kamar yadda muka saba.

"Muna yabo ga dukkan wadanda suka bamu shawara ta kowanne fanni kuma muna tabbatar da cewa za mu ci gaba da aikin habbaka jihar nan.

"Ina son yin amfani da wannan damar wurin kira ga abokan aikinmu da su bamu goyon baya wurin dauke nauyin da ya hau kanmu," tace.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bai wa mataimakin Akeredolu muhimmiyar shawara

An dakatar da 'yan majalisar biyar ne saboda rashin da'a da kuma take dokokin majalisar yayin da ake kokarin tsige tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

'Yan majalisar sun hada da: Labaran Abdul Masari, Bello Butubutu, Isyaku Ali, Garba Ya'u da Maje Gwangwazo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel