PDP ta bai wa mataimakin Akeredolu muhimmiyar shawara
- Jam’iyyar PDP ta shawarci mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi da ya yi murabus
- PDP ta bukaci hakan ne ganin cewa Agboola ya bar jam’iyyar APC da aka zabesa a karkashinta
- Agboola dai sun raba jiha da gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu tun kafin ficewarsa daga APC
Jam’iyyar PDP ta shawarci mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi da ya yi murabus tunda ya bar jam’iyyar APC da aka zabesa a karkashinta.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Ayo Fadaka, ya bayyana hakan yayin zantawa a Sunrise Daily na gidan talabaijin din Channels.
Ya ce, kamata yayi Ajiyi ya yi abinda ya dace ta hanyar yin murabus hankali kwance tunda ba zai iya tafiya daya da gwamnan ba.
Kakakin jam’iyyar PDP ya kara da cewa, ya rage ga gwamnan da kuma jam’iyyar APC Ko za su ci gaba da zama da Ajayi a matsayin mataimakin gwamnan duk kuwa da sauya shekar da yayi.
“Akwai yuwuwar a tsigesa idan har suna ganin mataimakin gwamnan ya yi wani abinda bai dace ba,” Kakakin jam’iyyar PDP ya sanar.
“Kundun tsarin mulkin kasa cewa yayi, ga duk gwamnan da zai yi takara, dole ne ya samu mataimaki. Gwamnan ya zabi Agboola Ajayi, amma kuma a lokacin ba dan jam’iyyar PDP bane.
“Idan yana tunanin ba zai iya hakura ba, ba mu da wani tsimi ko dabara. Ya rage wa Ajayi da ya yi abinda zai tsira da mutuncinsa ta hanyar yin murabus idan ya ji ba zai iya yin aiki karkashin gwamnan ba.”
KU KARANTA KUMA: Inganta noma: FG ta fitar da N600bn don tallafawa manoma
Fadaka ya yi kira ga jiga-jigan jam’iyyun siyasa da ke da wata alaka da PDP da su dawo jam’iyyar. Ya kara da cewa PDP na matukar farin cikin karbar tsoffin ‘ya’yanta.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce yana farin cikin rikicin da ya barke a jam'iyyar APC.
Wike ya sanar da talabijin Arise a wata tattaunawa da suka yi. Ya ce yana farin cikin halin da jam'iyyar ke ciki da yadda Gwamna Obaseki na jihar Edo ya koma jam'iyyar PDP.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng