Gwamnatin jihar Jigawa ta umarci ma'aikata su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Jigawa ta umarci ma'aikata su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Jigawa ta kara daukan matakin sassauta dokokin da aka saka bayan bullar annobar korona bayan ta bukaci ma'aikatanta su koma bakin aiki a ranar Litinin mai zuwa, 6 ga watan Yuli, 2020.

Mohammed Badaru Abubakar, gwamnan jihar Jigawa ne ya sanar da hakan a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai.

A cewar gwamnan, umarnin komawa aikin ya shafi ma'aikatan da ke kan mataki na 12 zuwa sama ne kawai.

Dangane da bude makarantu a jihar, gwamna Badaru ya ce gwamnatinsa za ta sake duba yiwuwar bude makarantu duk da gwamnatin tarayya ta amince makarantu domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa.

Ya kara da cewa gwamnatin Jigawa za ta bude makarantun da ke fadin jihar bayann ta gamsu cewa yin hakan ba zai haifar da wata matsala ba.

Gwamnatin jihar Jigawa ta umarci ma'aikata su koma bakin aiki
Gwamnan jihar Jigawa; Badaru Abubakar
Asali: Twitter

A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta ce za a cigaba da rufe makarantun kananan yara da makarantun firamare da ke fadin kasar nan.

A sanarwar da ta fito kafin wannan, gwamnatin tarayya ta ce za a bude makarantu daga matakin firamare zuwa sakandire domin bawa daliban da ke shekarar karshe damar rubuta jarrabawa.

Sai dai, a cikin wata sanarwa da Dakta Sani Aliyu, jagoran kwamitin yaki da annobar korona a kasa, ya fitar a Abuja ya ce ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama 'yan bindigar da su ka kashe Dakta Audu bayan karbar N7.5m kudin fansa

"Ba za a bude makarantun kananan yara da makarantun firamare ba har sai sanarwa ta gaba," a cewarsa.

A baya Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta amince da bude makarantun firame da sakandire a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan taron da ya wakana tsakanin kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa (PTF) da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda gwamnatin tarayyar ta bayyana, azuzuwan da za su koma bakin karatun sun hada da:

1. Aji shida na dukkan makarantun firamare.

2. Daliban aji uku da na aji shida na makarantun sakandaren da ke fadin kasar nan.

Hakazalika, gwamnatin tarayyar ta amince da bude shige da fice tsakanin jihohin kasar nan, amma matukar ba a zarta lokutan doka ba.

Gwamnatin tarayyar ta kara da amincewa da sauka ta tashin jiragen sama a cikin fadin kasar nan kadai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel