Duniya mai yayi: Gwamna Nasir El-Rufai da Hadiza Isma a shekarun baya

Duniya mai yayi: Gwamna Nasir El-Rufai da Hadiza Isma a shekarun baya

Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta tuna baya yayin da ta fito da wani tsohon hotonta da maigidanta watau gwamna Nasir Ahmed El-Rufai.

Hadiza Isma El-Rufai ta fito da wannan hoto ne a dandalin sada zumunta na zamani na Twitter a ranar Asabar, 27 ga watan Yuni, 2020.

El-Rufai mai shekaru 60 ta bayyana cewa an dauki wannan hoto ne a lokacin Nasir El-Rufai ya na saurayi, bai riga ya aure ta ba tukuna.

Kawo yanzu fiye da mutane 1, 500 su ka yi yawo da hoton, inda mutum kusan 13, 000 su ka nuna cewa wannan tsohuwar ajiyar ta burge su.

Mai girma gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana game da dadadden hoton, ya ce sun yi wannan hoto ne bayan an sa masu rana.

“Tuna baya a shekarar 1984: Ni da wanda zan aura a lokacin kuma kashin sa’a ta, Hadiza Isma a ruwan Tiga, Kano.” Inji Malam El-Rufai.

KU KARANTA: Ba na cikin gwamnatin El-Rufai inji Mai dakinsa

Malam El-Rufai ya kara bayani: “A wajen bikin auren ‘yaruwarta, Fatima Isma-Abdullahi da amini na, Tijjani Mohammed Abdullahi.

Tsohon ministan babban birnin tarayya ya kare da godewa Ubangiji cewa: “Alhamdulillah!" Ya ce: "Dubi yadda lokaci ya ke gudu.”

Wani matashi mai suna Umar Sa'ad Hassan ya soki yadda Malam El-Rufai ya taba jikin sahibarsa a lokacin da ba su kai ga yin aure ba.

Isma El-Rufai ta maidawa matashin da ire-irensa martani da cewa Ubangiji mai rahama ne da jin kai, da nufin za a yafewa masu kure.

A 1985 Nasir El-Rufai ya auri Hadiza-Isma a Kano, ya fara haduwa da ita ne a makaranta a Zariya, an samu yara da-dama a tsakaninsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel