Takardun shaida: Kotu ta yi fatali da karar da aka shigar a kan Godwin Obaseki

Takardun shaida: Kotu ta yi fatali da karar da aka shigar a kan Godwin Obaseki

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Alkalin wani babban kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja, ya yi watsi da karar da aka shigar a kan gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a gabansa.

An zargi gwamnan da badakalar takardar shaidar karatu, amma ba a iya tabbatar da wannan zargi a kotu ba.

Rahotanni sun bayyana cewa Alkali Anwuli Chikere ne ya saurari shari’ar, kuma ya yi fatali da ita bayan wadanda su ka shigar da karar sun gaza bayyana a gaban kotu jiya.

A lokacin da Alkali mai shari’a Anwuli Chikere ya ambaci masu tuhumar Mista Godwin Obaseki da amfani da takardar shaidar digirin bogi, sai aka neme su aka rasa.

Wadanda aka ambata a shari’ar mai lamba ta FHC/ABJ/CS/553/2020 su ne Edobor Williams, Ugbesia Abudu Godwin, da kuma wani Amedu Dauda Anakhu.

Wadannan mutane uku sun jefi gwamnan na jihar Edo da amfani da takardar digirin bogi da sunan jami’ar tarayya da ke garin Ibadan, domin tsayawa takara a zaben 2016.

KU KARANTA: Jigon PDP zai bi 'Dan takarar APC a zaben Edo

Takardun shaida: Kotu ta yi fatali da karar da aka shigar a kan Godwin Obaseki
Mai girma Godwin Obaseki
Asali: UGC

Masu tuhumar mai girma gwamnan sun fadawa babban kotun tarayyar cewa laifin da ake zarginsa da shi ya ci karo da sashe na 182(1)(i) na kudin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A dalilin haka masu karar su ka roki kotu ta haramtawa Godwin Obaseki damar tsayawa takarar gwamna a zaben jihar Edo wanda za a yi a cikin watan Satumban nan mai zuwa.

Da aka yi zama domin a saurari wannan shari’a a jiya Litinin, 29 ga watan Yuni, 2020, wadannan mutane da lauyoyin da ke kare su ba su halarci zaman kotun ba.

Haka zalika mai girma Obaseki da kuma lauyan da ke kare sa, duk ba su halarci wannan zama ba. A karshe dole Anwuli Chikere ya yi watsi da wannan kara daga gaban kotunsa.

Hakan na nufin an wanke Mista Godwin Obaseki, zai iya tsayawa neman takara a zaben na Edo. Wannan na zuwa ne bayan ya zama ‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel