Shugabancin APC: Giadom ya mika wa Gwamna Buni jagoranci

Shugabancin APC: Giadom ya mika wa Gwamna Buni jagoranci

Tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Victor Giadom, ya mika karagar mulkin jam’iyyar ga shugaban kwamitin rikon kwarya, Gwamna Mai Mala Buni.

An yi bikin mika karagar mulkin a sakateriyar APC da ke Abuja a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni.

A jawabinsa, Giadom ya tabbatar wa da ‘yan kwamitin cewa a shirye yake ya bada goyon baya tare da aiki a matsayin kungiya don ganin tabbatuwar abinda jam’iyyar ta saka gaba.

Ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin kwamitin zababbabu na jam’iyyar da suka ceto ta daga halaka, Channels TV ta ruwaito.

A bangarensa, Gwamna Buni ya yayi kira ga fusatattun ‘yan jam’iyyar da su janye karar da suka mika ta junansu gaban kotu.

Shugabancin APC: Giadom ya mika wa Gwamna Buni jagoranci
Shugabancin APC: Giadom ya mika wa Gwamna Buni jagoranci Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Ya ce, “Ina kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar da su ji abinda shugaban kuma jagoranmu Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kan kira da yayi ga fusatattun ‘yan jam’iyyar da su janye kararrakinsu da suka kai juna gaban kuliya.”

Kamar yadda gwamnan jihar Yoben ya sanar, abubuwan da suka dinga faruwa a jam’iyyar APC a watanni kadan da suka gabata ba bakon abu bane ga kowacce jam’iyyar siyasa matukar ta kasaita.

Ya kara da cewa, rashin jituwar cikin gida ba sabon abu bane a kowacce jam’iyyar siyasa kuma jam’iyyar APC ba ta fita daban ba.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya za su san mataki na gaba na sassauta doka a ranar Talata

Gwamna Buni, wanda ya rantsar da kwamitin mutum 13, ya ce, “Lokaci ya yi da kwamitin nan za su fara aikin sasanci tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar a kowanne mataki.

“Mun yarda cewa, shawarar da kwamitin shugabannin jam’iyyar suka yanke na kafa wannan kwamitin na bayyana tushen sabon babi ga jam’iyyarmu mai daraja.”

A wani labarin kuma mun ji a baya cewa Wike ya sanar da hakan ga talabijin din Arise a wata tattaunawa da suka yi. Ya ce yana farin cikin halin da jam'iyyar ke ciki da yadda Gwamna Obaseki na jihar Edo ya koma jam'iyyar PDP.

Ya ce ba zai taba yi wa jam'iyyar APC fatan ta daina kura-kurai ba kuma cewa hakan zai bai PDP damar karbe mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel