'Yan bindiga sun tashi gari kacokan a jajiberin zaben kananan hukumomi a Taraba

'Yan bindiga sun tashi gari kacokan a jajiberin zaben kananan hukumomi a Taraba

A yayin da ya rage saura sa'o'i 24 a fara kada kuri'a a zaben kananan hukumomin jihar Taraba, wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar tsageranci ta kabilar Jukun ne sun tashi kauyen Afogba da ke yankin karamar hukumar Donga.

Mazauna kauyen sun ce mutum guda ya mutu yayin da wasu mutane uku suka samu raunuka yayin harin wanda aka kai da duku-dukun safiyar ranar Litinin.

Wani mazaunin kauyen, Mista Livinus Aka, ya ce, "sun bullo daga yankin Tunari, sun kawo mana hari. Mun gudu mun bar gidajenmu bayan mun ji a jikinmu cewa zasu kawo mana hari.

"Sun kashe mutum guda bayan ya yi kuskuren bi ta hanyar da su ka biyo saboda lokacin akwai sauran duhu. Sun raunata mutane uku, yanzu haka ma suna asibiti," a cewarsa.

'Yan bindiga sun tashi gari kacokan a jajiberin zaben kananan hukumomin a Taraba
'Yan bindiga sun tashi gari kacokan a jajiberin zaben kananan hukumomin a Taraba
Asali: UGC

Sai dai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, David Misal, ya ce bai samu labarin kai harin ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Misal ya yi alkawarin cewa zai tuntubi manema labarai da zarar ya tabbatar da faruwar lamarin.

DUBA WANNAN: Kwamitin yaki da annobar korona ya sake komawa gaban Buhari da sabbin bayanai

The Jukun and Tiv ethnic groups in Taraba have been embroiled in a bloody clash in the southern part of the State since April 1, 2019, with the crisis now escalating to Bali and Gassol Local Government Areas in the central zone.

Jihar Taraba ta dade tana fama da rikicin kabilanci a tsakanin kabilun Tiv da Jukun a kudancin Taraba, wanda kuma yanzu haka ya ke kara tsamari a kananan hukumin Bali da Gassol da ke tsakiyar jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel