Sojoji 4, 918 sun kammala horo a makarantar kananan Soji da ke Zariya

Sojoji 4, 918 sun kammala horo a makarantar kananan Soji da ke Zariya

- Sojoji sun samu karin Dakaru 4, 900 da za su taimaka wajen yaki da rashin tsaro

- A karshen makon da ya gabata aka yaye Runduna 4, 918 a makarantar soji a Zariya

- Janar Lamidi Adeosun ya wakilci Janar Tukur Buratai wajen yaye Dakarun kasar

A ranar Lahadi, 29 ga watan Yuni, 2020, shugaban hafsun sojin Najeriya, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce sojojin kasa sun shirya shawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi.

Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi wannan bayani ne a wajen bikin yaye kananan sojojin kasa a makarantar soji ta Zariya. A karshen makon nan ne sahun sojoji na 79 su ka kammala daukar horo.

Shugaban sojojin kasan ya ce Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro a dalilin rikicin ‘yan ta’addan Boko Haram, ta'adin 'yan bindiga, garkuwa da mutane da wasu laifuffuka a fadin kasar.

Shugaban harkokin tsare-tsare da shirye-shirye a gidan sojin kasa, Laftana Janar Lamidi Adeosun shi ne wanda ya wakilaci hafsun sojin a wajen wannan gagarumin biki da aka yi a jihar Kaduna.

KU KARANTA: Sojoji sun yi wa 'Yan bindiga lahani

Sojoji 4, 918 sun kammala horo a makarantar kananan Soji da ke Zariya
Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai
Asali: Facebook

Lamidi Adeosun ya ce da wadannan sababbin sojoji har 4, 198 da aka yaye, matsalar rashin tsaro zai zama tarihi a Najeriya.

Hafsun ya jinjinawa dakarun da su ka kammala daukar horo a makarantar kananan sojojin, sannan ya yabawa sashen horaswar gidan soja da ya yi kokari wajen ganin an horaswa Najeriya da wadannan sojoji.

Janar Lamidi Adeosun ya yi wa sababbin dakarun da jami’an makarantar alkawarin cewa hukuma za ta dage game da abin da ya shafi jin dadi da walwalarsu domin su yi aiki da kyau.

Haka zalika Lamidi Adeosun ya bayyana cewa makarantar za ta cigaba da samun gudumuwa daga gidan soja. Adeosun duk ya yi wannan jawabi ne a madadin Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel