Ina matukar farin ciki da rikicin APC - Gwamna Wike

Ina matukar farin ciki da rikicin APC - Gwamna Wike

- Gwamna ya nuna farin cikinsa a kan yadda jam' iyyar APC mai mulki ta tsinci kanta cikin rikici

- Ya ce yana farin cikin halin da jam'iyyar ke ciki da yadda Gwamna Obaseki na jihar Edo ya koma jam'iyyar PDP

- Wike ya ce ba zai taba yi wa jam'iyyar APC fatan ta daina kura-kurai ba kuma ewa hakan zai bai PDP damar karbe mulki

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce yana farin ciki kan rikicin da ya barke a jam'iyyar All Progressives Party (APC).

Wike ya sanar da hakan ga talabijin din Arise a wata tattaunawa da suka yi. Ya ce yana farin cikin halin da jam'iyyar ke ciki da yadda Gwamna Obaseki na jihar Edo ya koma jam'iyyar PDP.

Ya ce ba zai taba yi wa jam'iyyar APC fatan ta daina kura-kurai ba kuma cewa hakan zai bai PDP damar karbe mulki.

"Ina farin ciki a kan rikicin APC. Ba matsala ta bane don haka babu bukatar su samu hadin kai," gwamnan yace.

Ina matukar farin ciki da rikicin APC - Gwamna Wike
Ina matukar farin ciki da rikicin APC - Gwamna Wike Hoto: Transport Day
Asali: UGC

"Idan za ku tuna mun samu rikici zamanin Ali Modu Sheriff kuma APC ta yi murna da hakan. Ina fatan rikicin ya ci gaba. Mun sake kwace wata jiharsu. Abun takaici ne yadda yanzu APC ta sauya daga jam'iyyar siyasa.

"Ina fatan jam'iyyata ta samu mulkin kasar nan. Saboda hakan bana fatan rikicin APC ya tafi. Ina fatan su ci gaba da kura-kurai sannan jam'iyyata ta ci gaba da girma."

Gwamnan ya ce bashi da wata damuwa da Obaseki ya karbi tikitin takarar gwamnan jihar Edo a karkashin inuwar PDP amma ya shawarci cewa a dinga tafiya da sauran 'yan jam'iyyar.

Ya ce dole ne 'yan jam'iyyar na jihar su hada kansu sannan su yi aiki tukuru don cin zaben mai zuwa da kuma gujewa fadawarsu cikin matsala kamar jam'iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun mamaye gidan marigayi Ajimobi

"Tafiya tare da jama'a ba yana nufin a basu kudi bane. Wannan kuskure ne da wasu ke yi. Yana nufin sauraronsu, rokarsu tare da nuna musu cewa jam'iyya don su aka yi ta," Wike yace.

Za a yi zaben gwamnoni na jihar Edo a ranar 19 ga watan Satumban 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng