Boko Haram: Dakaru 9 sun rasa ransu a sabon hari a Borno

Boko Haram: Dakaru 9 sun rasa ransu a sabon hari a Borno

A kalla dakarun sojin Najeriya tara ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon harin 'yan Boko Haram.

Mayakan kungiyar 'yan ta'addan sun halaka sojin ne bayan da suka dauki motarsu suna raka matafiya daga Maiduguri zuwa garin Damboa, wata majiya tare da jami'an tsaro suka tabbatar.

Wannan ne karo na farko da sojojin da ke raka matafiya suka fuskanci hari daga wurin mayakan.

Damboa na da nisan kilomita 85 daga kudancin Maiduguri. Ta kasance daya daga cikin kananan hukumomin da suka fi fuskantar hari daga mayakan ta'addancin a jihar Borno.

Duk da sojojin ne ke bai wa garin kariya daga 'yan ta'adda tare da tsare manyan hanyoyin, Damboa ce babbar hanyar shiga karamar hukumar Chibok a jihar.

A kowacce rana, ababen hawa da ke shige da fice a garin na taruwa don samun rakiyar sojojin. Wadannan dakarun ke rakiya ga matafiya da ke tahowa daga Maiduguri, Chibok ko Damboa.

A ranar Asabar, matafiya daga Maiduguri sun fuskanci hari daga yan ta'addan da suka mayar da hankali wurin tarwatsa motar sojojin.

Boko Haram: Dakaru 9 sun rasa ransu a sabon hari a Borno
Boko Haram: Dakaru 9 sun rasa ransu a sabon hari a Borno Hoto: Dabatv
Asali: Twitter

"Ya faru wurin karfe 2 na rana. Lokacin tawagar sun isa kauyen Abbari," wani matafiyi da ya tsallake rijiya da baya ya sanar.

"Mun kusa shiga Damboa a yayin da muka ji wani sauti kuma kafin mu san abinda ke faruwa, mun ga motar sojojin ta kama da wuta. Daga nan sai harbe-harbe muka fada ji."

Wanda ya samu tserewan mai shekaru 37 ya bukaci a boye sunansa saboda tsaro, ya ce dukkan matafiyan da ke ababen hawa sun sauka inda suka dinga gudu.

"Na san sojoji da yawa sun mutu saboda harbin da suka dinga yi wa abun hawar dakarun."

Wani shugaban jami'an tsaron farar hula, Bunu Malam, ya tabbatar da aukuwar hakan ga jaridar Premium Times. Ya ce sojoji tara ne suka rasu sakamakon harin.

KU KARANTA KUMA: Katsina: Yadda 'yan gudun hijira suka dinga kuka bayan Masari ya kai ziyara

"Mun rasa dakaru tara a yayin da suke rakiya ga matafiya daga Maiduguri zuwa Damboa," yace.

"Maharan sun tsere da motar sintirin 'yan sa kai wadanda ke daga cikin tawagar masu rakiyar."

Majiyar ta ce maharan basu taba masu tafiyar ba da yake fararen hula ne.

Har a halin yanzu rundunar sojin baya yi tsokaci a kan al'amarin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel