Yanzu-yanzu: Babu ɓaraka tsakanin Buhari da Tinubu - Fadar Shugaban Ƙasa
Babban mai bai wa shugaban kasa shawara a kan yada labarai, Garba Shehu, ya ce Manjo Janar Muhammadu Buhari da jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, na nan tare.
Fadar shugaban kasa ta yi kira ga masu hasashe da su dakata da yada labarai marasa tushe, jaridar The Punch ta ruwaito.
Shehu ya sanar da hakan ne a wata takardar da ya fitar yayin martani ga rahotannin da suka shafi sauke 'yan kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar da shugaban kasar yayi.
Ya rubuta, "Domin bada bayani kai tsaye, wajen kafa jam'iyyarmu mai daraja da bada shugabancinta, shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Tinubu ne a kan gaba.
"Sun kasance masu tabbatar da tsarin damokaradiyya tare da bukatar 'yan kasa ba siyasar bangare ba.
"Har a yanzu suna tare da juna. Dangantakarsu na nan da karfi kamar yadda take a da. Su kadai suka san yadda suka gina dangatakarsu tare da kiyayeta."
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce amfanin amsa bukatar da kwamitin shugabannin jam'iyyar APC suka mika wa Buhari, shine janye rikicin cikin gidan da ya addabi jam'iyyar.
Shehu ya ce jam'iyyun adawa na yin amfani da duk wata dabararsu da kuma magoya bayansu a kafafen sada zumuntar zamani don shiga tsakanin shugabannin biyu amma sun kasa.
KU KARANTA: Alburusai 818 cikin shinkafa: Wasu mata 3 sun fada komar Yan sanda (Bidiyo)
A wani labari na daban, jagora a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya ce bai yanke shawarar yin takarar kujerar shugaban kasa ba a shekarar 2023 akasin hasashen da wasu ke yi.
Ya ce a halin yanzu ya fi mayar da hankali ne a kan kallubalen tattalin arziki da kasar ce fuskanta a halin yanzu da matsalar annobar coronavirus da mutane ke fuskanta.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, a karo na farko, ya yi magana a kan rushe kwamitin gudanarwa ta Adams Oshiomhole na jam'iyyar ta All Progressives Congress (APC).
A ranar Alhamis ne aka rushe NWC din ta Oshiomhole yayin taron Kwamitin Zartarwa, NEC, na gaggawa da aka kira. Taron ya samu hallarcin Shugaba Buhari, mataimakinsa Osinbajo da wasu jiga-jigan jam'iyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng