Yabon PDP: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a cikin martanin da ya mayar ma sa

Yabon PDP: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a cikin martanin da ya mayar ma sa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya mayarwa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, martani a kan kalamansa na yabon jam'iyyar PDP.

A ranar Alhamis ne Atiku, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019, ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa; "PDP ce kyakyawan misali na jam'iyyar da zata kare martabar siyasa a Najeriya saboda ta na aiki da tsari da biyayya ga kundin tsarin mulki.

"Ina fatan za mu cigaba da kare doka kamar yadda mu ka saba, ina fatan sauran jam'iyyun siyasa da ke Najeriya zasu koyi darasi tare da kwaikwayon jam'iyyar PDP.

"Duk jam'iyyar da ta gaza aiki da dokokinta, ba zata iya aiki da dokokin Najeriya ba," a cewar Atiku.

Atiku ya bayyana hakan ne jim kadan bayan jam'iyyar APC ta rushe kwamitinta na gudanarwa (NWC) sakamakon rigingimun shugabancin da ta fada.

Atiku ya tsaya neman tikitin takarar shugaban kasa tare da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a jam'iyyar APC a shekarar 2014.

Yayin zaben fidda dan takarar da aka yi a jihar Legas, Atiku ya zo na uku, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zo na biyu.

Yabon PDP: Sule Lamido ya ci gyaran Atiku a cikin martanin da ya mayar ma sa
Atiku, Lamido da Kwankwaso
Asali: Twitter

A cikin watan Disamba na shekarar 2017, Atiku ya koma tsohuwar jam'iyyarsa PDP inda ya yi takarar shugaban kasa a 2019.

A martanin da ya mayar, Sule Lamido ya nuna rashin amincewa da Atiku tare da bayyana kalamansa a matsayin 'holoko'.

DUBA WANNAN: Zamfara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan bindiga, sun saki bam a kogon Hassan Tagwaye a dajin Damborou

"Jam'iyyar PDP ba ta da tarbiyar yin irin wannan furuci. Idan mu ka yi duba da irin halayenmu a matsayinmu daidaikun mutane zamu gane cewa wadannan kalamai 'holoko'ne. Ya kamata mu zama masu tuhumar kanmu," a cewar Lamido.

Sule Lamido na daga cikin mutane 11 da Atiku ya kayar yayin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda aka yi a garin Fatakwal, jihar Ribas, a shekarar 2018.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Atiku da Lamido na daga cikin manyan 'ya'yan jam'iyyar PDP daga arewa da ke harin takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel