Rushe shugabannin APC: Mambobin kwamitin NWC na Osiomhole sun garzaya kotu

Rushe shugabannin APC: Mambobin kwamitin NWC na Osiomhole sun garzaya kotu

Mambobin kwamitin gudanarwa na Adams Oshiomhole (NWC) sun yanke shawarar daukar matakin doka kan hukuncin majalisar koli da gudanar da harkokin jam’iyyar (NEC) na rushe shugabanin jam’iyyar na kasa.

NEC a lokacin wani taron gaggawa na yanar gizo ta yanke hukunci ciki harda rushe shugabancin jam’iyyar na kasa da kuma kafa kwamitin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Sai dai kuma, da yake martani kan ci gaban, wani mamba a kwamitin NWC na Oshiomhole ya fada wa jaridar Daily Sun cike da kwarin gwiwar cewar an kammala shiri domin daukar mataki na doka.

Rushe shugabannin APC: Mambobin kwamitin NWC na Osiomhole sun garzaya kotu
Rushe shugabannin APC: Mambobin kwamitin NWC na Osiomhole sun garzaya kotu Hoto: The Nation
Asali: UGC

Da yake caccakar hukuncin NEC, mamban ya dage kan cewa babu gurbin kwamitin rikon kwarya a kundin tsarin jam’iyyar mai mulki, inda ya bayyana cewa suna da hujjoji da yawa na take doka da aka yi a hukuncin NEC.

“Ba da jimawa ba za mu fitar da jawabi amma mun yanke shawarar zuwa kotu domin daukar mataki na doka a kan hukunin NEC musamman da ya shafi rushemu.

KU KARANTA KUMA: Mai Mala Buni ya fadi ta hanyar da zai warware rigingimun APC

"Kwarai mun san cewa Oshiomhole na da nashi kura-kuran, amma duba ga dukkanin ayyukan alkhairi da ya yi wajen gyara jam’iyyar, shin bai cancanci a karrama shi ba ta hanyar fada mai ya yi murabus?” ya tambaya.

A baya mun ji cewa hugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci 'yan jam'iyyar APC da su janye duk wasu kararrakin juna da suka shigar a kotu.

Ya yi kira garesu da su sasanta tsakaninsu tare da jan kunnen cewa fada-fadace zai iya tarwatsa jam'iyyar APC.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin taron kwamitin shugabannin jam'iyyar da aka yi ta yanar gizo a Abuja.

Ya jaddada cewa duk nasarar jam'iyyar za ta iya rikidewa zuwa rashin nasara. Ya shawarcesu da su mayar da hankali wurin hada kan jam'iyyar.

Shugaba Buhari ya matukar damuwa a kan yanayin shugabanci da sauyawar biyayya a jam'iyyar wacce yace ta sa jama'a na wa jam'iyyar ba'a.

Kamar yadda yace, akwai rikici tsakanin masu rike da shugabancin jam'iyyar a matakin kasa yayin da APC take tantama a kan wasu ikirarin shari'a tare da hukunce-hukunce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel