Katsina: Jami'in tsaro da mutum shida sun rasa ransu a sabon hari
- Yan bindiga sun halaka mutum shida a safiyar Alhamis, 25 ga watan Yuni, bayan sun kai hari kauyuka biyu na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina
- Daga cikin wadanda aka kashe harda jami'in tsaro daya
- Jama'a da yawa a kauyen sun samu raunika sannan mata biyu masu ciki sun samu harbi daga bindiga
Wani jami'in tsaro tare da mazauna kauye shida ne suka rasa ransu a safiyar Alhamis, 25 ga watan Yuni, sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kauyuka biyu na karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Mutum uku-uku aka kashe a kauyen Kanga da Kanawa.
Wani jami'in tsaro ya rasu bayan ya je ceton mazauna kauyen daga hannun 'yan bindigar.
Jama'a da yawa a kauyen sun samu raunika sannan mata biyu masu ciki sun samu harbi daga bindiga. Tuni aka mika su babban asibitin Danmusa don karbar taimakon gaggawa.

Asali: UGC
A yayin tabbatar da harin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce wurin karfe 2 na dare ne 'yan bindigar suka kai hari kauyukan tare da kashe mutum 6 da kuma raunata mutum 5, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
"A kalla 'yan bindiga sama da 10 ne suka kai harin. Jami'an mu sun je amma sai suka fatattako su sannan aka kashe jami'i daya.
"Mun sake tura jami'an tsaro yankin don inganta tsaro tare da damke maharan," ya kara da cewa.
KU KARANTA KUMA: Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya'
A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa yan sandan birnin tarayya Abuja sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane, Bello Saleh na kauyen Dobi da ke karamar hukumar Gwagwalada da aka dade ana nema ruwa a jallo.
A sanarwar da kakakin rundunar, DSP Anjuguri Manzah ya fitar, ya ce an kama wanda ake zargin ne a mabuyarsa da ke kauyen Paiko Kore na karamar hukumar Gwagwalada.
DSP Manzah ya ce wanda ake zargin da 'yan tawagarsa sun harbe wani Ejike Idoko mazaunin kauyen Dobi har lahira a yayin da ya yi kokarin hana su tafiya da matarsa mai juna biyu.
Ya ce ana cigaba da kokarin ganin an kamo sauran 'yan tawagar na Saleh tare da kwato bindigun da ke hannunsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng