Miliyan goma: Nyesom Wike zai ci tarar ma su bikin aure a Ribas
Gwamnatin jihar Ribas ta fitar da sabbin tsare - tsare a kan gudanar da shagulgulan bikin aure tare da saka tarar miliyan goma a kan duk wanda aka samu sun sabawa doka.
Da ya ke sanar da hakan, kwamishinan yada labarai da sadarwa, Fasto Paulinus Nsirim, ya ce an samar da sabbin tsare - tsaren ne yayin taron majalisar zartarwa (NEC) na jihar Ribas wanda gwamna Nyesom Wike ya jagoranta.
Ya ce ma su niyyar aure za su rubuta takardar sanarwa zuwa ofishin gwamna ta hannun ofishin kwamishinan walwala da tallafi.
A cewar Nsirim, dole ma su niyyar aure su bayar da dukkan bayanai da suka shafi bikin aurensu, wanda suka hada da wurin biki, adireshi, sunayen ma'aurata da lambobin wayarsu.
Kwamishinan ya kara da cewa akwai sabuwar doka da ta bukaci duk wanda za su binne mamaci su aika takardar sanarwa mai dauke da sunaye da adireshin mutanen da zasu halarci jana'aizar.
Nsirim ya ce gwamnati ba za ta bayar da izinin yin biki ko binne gawa ba matukar babu sunaye, adireshi, da lambobin wayar wadanda abin ya shafa ba.
Ya ce mutanen da doka ta amince su taru a wurin bikin aure kar su wuce mutane 50, hakan ya hada har da dangin ma'aurata, kuma dole su saka takunkumin fuska, sannan su bawa juna nisan kilomita biyu.
DUBA WANNAN: APC: Bayan samun goyon bayan Buhari, Giadom ya bayyana wata damuwarsa
A cewarsa, duk auren da za a daura a Coci dole a yi hakan tsakanin karfe 9:00 na safe zuwa 12:00 na rana, yayin da taron bukukuwan gargajiya za a gudanar da su a tsakanin karfe 4:00 na yamma zuwa karfe 7:00 na yamma.
Kwamishinan ya kara da cewa dole a samar da ruwa da sabulu a wurare uku domin wanke hannu a wurin taron biki.
Kazalika, ya bayyana cewa dole a yi feshin maganin kashe kwayoyin cuta a wurin da aka kammala taron biki, sannan doka ta haramta taron cin abinci bayan daurin aure domin takaita yaduwar kwayar cutar korona.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng