Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya'

Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya'

- Wani mai hakar ma'adanai a kasar Tanzania ya yi gam da katar inda ya zama miloniya a dare daya

- Ya yi nasarar hako wasu irin duwatsu guda biyu wanda ba a samunsu a duniya sosai

- Sanilu Laizer ya samu sama da dala miliyan 3.4 bayan ya siyar da duwatsun masu tsada

Wani karamin mai hako ma'adanai a kasar Tanzania ya zama miloniya a dare daya bayan siyar da wasu duwatsu da ya yi a kasar.

Saniniu Laizer ya samu dala miliyan 3.4 (N1,321,818,000) daga ma'aikatar hako ma'adanai ta kasar bayan samun duwatsun masu nauyin 9.2kg da 5.8kg.

Kamar yadda rahoton BBC ya bayyana, Laizer ya hako duwatsun ne a makon da ya gabata amma ya siyar dasu a ranar Laraba, 24 ga watan Yunin 2020 a yayin wani bikin baje-kolin kasuwanci da aka yi a yankin Arewacin Manyara.

Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya'
Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya' Hoto: BBC
Asali: UGC

"Na jajirce tare da mayar da hankali. Hakan ne babban sirri na, ina godiya a gareku," ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Mutumin mai shekaru 52 yana da mata hudu da yara sama da 30. Ya ce zai yanka Sa daya don murna.

Ya ce yana shirin bude makaranta da rukunin shagunan kasuwanci a yankin Simanjiro na Manyara.

Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya'
Yadda wani mutum mai 'ya'ya 30 ya zama miloniya a 'dare daya' Hoto: BBC
Asali: UGC

"Zan gina babban kanti da kuma makaranta kusa da gidana. Akwai matalauta da basu iya biyan kudin makarantar 'ya'yansu.

"Ban yi karatu ba amma ina so na tafi da kasuwancina ta kwararriyar hanya," yace.

KU KARANTA KUMA: APC NEC: Karfe 12 na rana Buhari zai shiga taron jam'iyya

A 2015, John Magufuli ya yi alkawarin bada kariya ga bangaren hako ma'adanai tare da habaka kudin shigar kasar. Ya kira Laizer inda ya taya shi murna.

"Wannan ne amfanin kananan mahaka ma'adanai kuma hakan na nuna cewa Tanzania na da tarin arziki," shugaban kasar yace.

A 2017, ya umurci rundunar soji da ta gina bango mai 24km kewaye da bagiren da ake ganin shine wuri guda da ake samun duwatsun a duniya, sashi mai 4km a kafar Mt Kilimanjaro.

Bayan shekara guda sai ma’aikatar ma’adinai ta Tanzania ta samu Karin kudaden shiga.

Hakan ya kasance ne sakamakon bangon da aka gina wanda ya hana fasa kauri.

Ana samun duwatsun ne a arewacin Tanzania kawai kuma ana amfani da su wajen yin abun ado. Ya kasance duwatsu da ba a cika gani ba a duniya.

Sai dai kuma, wani masanin ma’adinai ya yi kiyasin cewa samunsu zai yi karanci a shekaru 20 masu zuwa.

Duwatsun na da kaloli daban-daban kama daga kore, ja, launin shuni da uwan bula kuma iya kyan kalar ko haskenta, iya tsadar sa.

Kafin yanzu nauyin dutsen mafi girma da aka hako ya kasance 3.3kg.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel