NEC: Gwamnonin APC su na so a zauna, ka da Shugaba Buhari ya je - Farfesa Sagay

NEC: Gwamnonin APC su na so a zauna, ka da Shugaba Buhari ya je - Farfesa Sagay

Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Bagudu, wanda shi ne shugaban gwamnonin jam’iyyar APC, ya bayyana abin da ya sa shi da abokan aikinsa a APC su ke kiran ayi zaman majalisar NEC.

Jaridar Premium Times ta rahoto Abubakar Bagudu ya na cewa gwamnonin APC su na so ayi wannan zama ne domin shawo kan rigimar da ake fama da ita wanda ta ki ci, ta ki cinyewa.

Shugaban gwamnonin jam’iyyar mai mulki ya ce su na neman hanyar kawo zaman lafiya ne a APC. Sai dai ana tunanin cewa gwamnoni 7 ne kawai su ke da wannan ra’ayi a jam’iyyar.

A wani bangare guda kuma, Farfesan shari’a, Itse Sagay SAN, ya ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar kauracewa wannan taro na NEC da Victor Giadom ya kira a yau Alhamis.

Kamar yadda jaridar The Nation ta fitar da rahoto, Farfesa Itse Sagay ya bada hujjoji akalla uku na shari’a da su ka sa bai kamata shugaban kasar ya hallara wajen wannan taro na yau ba.

Na farko Victor Giadom bai da hurumin da zai dare kan kujerar shugaban jam’iyya domin kuwa ba ya kan layin wadanda za su gaji Adams Oshiomhole a APC, a cewar Masanin shari’ar.

KU KARANTA: Giadom ne ya dace ya rike Jam'iyyar APC - Buhari

NEC: Gwamnonin APC su na so a zauna, ka da Shugaba Buhari ya je - Farfesa Sagay
Farfesa Itse Sagay
Asali: Facebook

Ya ce: “Abin ya ba ni mamaki, ta ina mataimakin sakataren jam’iyya zai sa burin zama shugaban jam’iyya a lokacin da akwai mataimakan shugabannin jam’iyya da mataimakansu?”

Dalili na biyu kuma shi ne, wa’adin umarnin da kotu ta bada na cewa Giadom ya yi aiki a matsayin shugaban rikon kwarya a APC, ya wuce. Farfesan ya ce wa’adin ya shude yanzu.

“Na biyu ya na dogara ne da umarnin da kotu ta bada a Maris. Umarnin su na aiki ne na tsawon kwanaki 14. Ya zo cikin watan Yuni ya ce kotu ta tsawaita wa’adin umarnin da ya wuce.”

“Abin gaba daya akwai kwamacala. Ban taba jin abin da ya kai wannan muni ba.” inji Sagay.

“Na uku shi ne akwai bukatar a bada sanarwar kwanaki bakwai kafin a shirya taron NEC. Giadom ya bada kwanaki uku ne kawai.”

Don haka Farfesan ya ba Buhari shawarar gujewa taron da Victor Giadom ya kira. Sai dai tuni shugaban kasar ya fito ya nuna goyon bayansa ga Giadom, ya ce shi ya dace ya rike APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel