Wata sabuwa: Akwai yuwuwar APC ba za ta fito takara ba a zaben Ondo - INEC

Wata sabuwa: Akwai yuwuwar APC ba za ta fito takara ba a zaben Ondo - INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewa akwai yuwuwar jam'iyyar APC ba za fito takara ba a zaben gwamnonin da za a yi a jihar Ondo a watan Oktoba.

Hakan ya biyo bayan wasu rashin daidaituwa da ta gano a jam'iyyar bayan ta sauya lokacin zaben fidda gwaninta.

A wata wasika mai taken "Sanarwa a kan yadda za a yi zaben fidda gwani" wacce aka mikata ga sakataren jam'iyyar APC na kasa bayan sakatariyar hukumar, Rose Oriaran-Anthony ta saka hannu, wasikar ta yi magana a kan zaben fidda gwani.

Wannan ta ce ya ci karo da dokokin INEC a kan yadda za a yi zaben fidda gwani, jaridar The Sun ta ruwaito.

Wata sabuwa: Akwai yuwuwar APC ba za ta fito takara ba a zaben Ondo - INEC
Wata sabuwa: Akwai yuwuwar APC ba za ta fito takara ba a zaben Ondo - INEC Hoto: The Sun
Asali: UGC

Wasikar ya ce, "Hukumar ta gano cewa tsarin zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da za a yi a ranar 20 ga watan Yuli ya samu saka hannun sakataren jam'iyyar na kasa ne kadai.

"Wannan ya ci karo da takarda ta 4.4 ta dokokin hukumar a kan tsarin zaben fidda gwani inda ta bukaci shugaban jam'iyyar da sakatare su saka hannu a kai.

"Don haka, ana shawartar jam'iyyarku da ta bayar da cikakken sanarwar da ya kamata kan gudanarwar zaben fidda gwaninta na gwamnan jihar Ondo kamar yadda tsarin zaben ya tanadar."

KU KARANTA KUMA: Yadda tela ya yaudari yara mata 2 da takunkumin fuska yayi musu fyade

A wani labarin kuma, mun ji cewa rikicin jam’iyyar APC a jihar Ekiti ya dauki sabon salo a ranar Laraba bayan zargin yunkurin tsige mai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan harkokin siyasa, Sanata Babafemi Ojudu ya tashi a tutar babu.

Shugabannin jam’iyyar da jami'an unguwa ta 8 na karamar hukumar Ado ekiti sun tsallake kwamitin gudanar da ayyuka na APC na jihar inda suka yi yunkurin dakatar da Ojudu a kan rashin biyayya.

Hadimin shugaban kasar da Gwamna Kayode Fayemi sun taba rikici bayan da hadimin shugaban kasar ya zargi gwamnan da rashin aiki tare da salon mulki na kama-karya a jam’iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel