Sojoji sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a Katsina

Sojoji sun ceto mutane 6 da aka yi garkuwa da su a Katsina

A jiya Talata ne rundunar dakarun sojin kasa, ta kubutar da mutum shida daga tarkon 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Shugaban bataliyar rundunar dakaru ta 17, Birgediya Janar W.B Idris, shi ne ya gabatar wa da gwanatin jihar mutane shidan da suka ceto.

Manjo Emmanuel Adebayo, wanda ya wakilci Birgediya Janar Idris, ya ce sun samu nasarar ceto mutum 6 daga cikin 11 da 'yan daban daji suka yi garkuwa da su.

Ya ce kawo yanzu, rudunar sojin bata iya gano inda ragowar mutane 5 ba da suka fada tarkon masu garkuwa.

Sai dai ya bai wa al'ummar jihar Katsina tabbacin cewa, za su kara kaimi wajen ci gaba da tsefe dazuzzuka domin binciko ragowar mutanen a duk inda masu tayar da zaune tsayen suka fake da su.

Rundunar sojin kasan Najeriya yayin aikin ceto
Rundunar sojin kasan Najeriya yayin aikin ceto
Asali: Twitter

Da ya ke karbar mutanen da aka ceto, sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya yaba wa kwazon dakarun sojin musamman a fafutikar da suke yi na kawo karshen ta'addanci a jihar.

Sakataren gwamnatin wanda babban sakataren dindindin a ofishinsa Suleiman Yakubu Safana ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta gamsu da himmar dakarun sojin.

Kazalika tana mai fatan Allah ya taimaki rundunar sojin wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta a jihar, yankin Arewa da kuma kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya za ta yanke shawara kan dokar hana zirga-zirga a mako mai zuwa - PTF

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an danka mutanen da aka ceto a hannun dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar karamar hukumar Danmusa, Alhaji Dan Musa, domin ya mika su ga 'yan uwansu.

Rahotanni sun bayyana cewa, a 'yan kwanakin nan, dakarun sojin kasan Najeriya na ci gaba da fadi-tashin ceto mutanen da suka fada tarkon masu ta'addanci a jihar Katsina.

Ko a makon da ya gabata, sun ceto wasu mutum biyu daga hannun masu garkuwar da mutane a karamar hukumar Batsari ta jihar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Talata babban hafsan Sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Baba Abubakar ya bayyana cewa, an tura karin jirage masu saukar angulu biyar jihar Katsina.

AM Abubakar ya ce an tura jiragen ne domin karfafa yaki da ta'addanci a jihar da kuma sauran jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel