Dalilan da suka sa na tsaya wa Maina - Sanata Ndume

Dalilan da suka sa na tsaya wa Maina - Sanata Ndume

Shugaban kwamitin rundunar soji na majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ali Ndume, ya ce ya yanke hukuncin tsayawa don karbar Abdulrasheed Maina ne saboda alkawarin da yayi na wakiltar dukkan jama'ar mazabarsa komai ruwa ko rana.

Ndume ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja. Ya ce sai da ya dauki watanni shida kafin ya amince.

Tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina ya shiga hannun jami'an tsaro bayan zarginsa da ake da sama da fadi a kan dukiyar hukumar.

Sanatan mai wakiltar mazabar Borno ta kudu ya ce wannan babban hukunci ne ya yanke.

Dalilan da suka sa na tsaya wa Maina - Sanata Ndume
Dalilan da suka sa na tsaya wa Maina - Sanata Ndume Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Ndume ya ce: "Na dauki tsawon watanni shida kafin in amince da tsayawa Maina bayan an bada belinsa.

"Da farko dai sharadin belinsa ya hada da Sanata mai ci a yanzu ya tsaya masa kuma an yi sa'a nine a matsayin.

"Na biyu kuwa shine yadda kullum rashin lafiyarsa ke kara kamari kuma yana bukatar agajin masana kiwon lafiya.

"Na uku kuwa shine laifinsa wanda ake iya bada beli ne sai na karshe, ba ina bukatar kotu ta sakesa bane tare da wankesa. Za a hukunta shi idan aka kama shi da laifi.

"A gaskiya da kyar na amince. Na amince ne saboda ina wakiltar jama'a ta yadda ya dace, komai rintsi da tsanani."

A wani labari na daban, mun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa 'yan majalisar tarayya da masu manyan mukamai a kasar nan ne ke morar albashi mai tarin yawa amma talakawan Najeriya ke cikin wani hali.

Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi sun yi gaskiya a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya cike da tsada wanda yace ba dole bane hakan ya ci gaba.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa muka tura jami'ai babban ofishin APC - NPF

Ndume ya sanar da hakan ne yayin martani ga Osinbajo da Sanusi yayin tattaunawa a kan daidatuwar tattalin arziki bayan annobar korona.

A yayin da aka tattauna da Sanusi, ya bayyana cewa tsarin da ake bi na tafiyar da gwamnati a Najeriya na nuna cewa za ta durkushe kuma ya tambaya mataimakin shugaban kasa a kan abinda mukin nan ke yi don shawo kalubalen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel