Dalilin da yasa muka tura jami'ai babban ofishin APC - NPF

Dalilin da yasa muka tura jami'ai babban ofishin APC - NPF

- Hukumar yan sandan Najeriya ta sanar da dalilinta na garkame hedkwatar jam'iyyar APC na kasa

- Ta ce ta yi hakan ne don tabbatar da cewa ba a yi karantsaye ga doka ba sannan a shata layi tsakanin sassa biyu na jam'iyyar

- Kakakin rundunar, DCP Frank Mba ya ce zuwan jami'ansu babban ofishin jam'iyyar ba yana nufin za su rufe wurin bane

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta tura jami'anta babban ofishin jam'iyyar APC na kasa ne don tabbatar da cewa ba a yi karantsaye ga doka ba sannan a shata layi tsakanin sassa biyu na jam'iyyar, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba yasa hannu ta bayyana, zuwan jami'ansu babban ofishin jam'iyyar ba yana nufin za su rufe wurin bane. Sun yi hakan ne don gujewa rikicin da ka iya barkewa.

Dalilin da yasa muka tura jami'ai babban ofishin APC - NFP
Dalilin da yasa muka tura jami'ai babban ofishin APC - NFP Hoto: Channels TV
Asali: UGC

"Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun je babban ofishin jam'iyyar APC na kasa da ke Blantyre Crescent, Wuse II, Abuja.

"An tura su ne don kiyaye yuwuwar tashin hankali da take doka a wurin.

"Zuwan jami'an ba yana nufin rufe babban ofishin bane kamar yadda wasu suka yi tsammani.

"A don haka, ma'aikata da 'yan jam'iyyar za su iya ci gaba da hada-hadarsu ba tare da tsangwama ba," takardar tace.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wasu jami'an yan sanda sun kulle hedkwatar uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bisa umurnin Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IGP Mohammed Adamu, The Nation ta ruwaito.

Hakazalika an samu labarin cewa IGP na yan sanda zai gana da bangarorin kwamitin gudanarwan jam'iyyar a hedkwatar hukumar misalin karfe 1 na rana.

An tattaro cewa kwamishanan yan sandan birnin tarayya ya umurci babban jami'in tsaron hedkwatar ya bayyanawa mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar cewa babu wanda aka amince ya shiga harabar hedkwatar.

Majiya daga cikin jam'iyyar ya bayyana cewa an kulle hedkwatar ne domin baiwa shugaban yan sandan damar duba umurnin da kotu tayi da kuma wanda za'a bi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel