Da gangan sojoji suka harbe jami'an IRT don ceton Wadume - Shaida

Da gangan sojoji suka harbe jami'an IRT don ceton Wadume - Shaida

- Aminu Ahmed, makwabcin Bala Hamisu wanda aka fi sani da Wadume, ya ce da gangan sojoji suka harbe jami'an IRT don ceton Wadume

- Ya ce ya tabbatar da cewa Wadume ya shiga harkar garkuwa da mutane tun kafin jami'an tsaro su kama shi

- Sai dai ya ce Wadume ya bashi kyautar babur shiyasa yake ta kokarin shawo kan matsalarsa

Wani makwabcin Bala Hamisu wanda aka fi sani da Wadume, mai suna Aminu Ahmed, ya ce dakarun da ke karkashin Kaftin Tijjani Balarabe sun kashe 'yan sanda uku da farar hula biyu don samun kubutar da Wadume daga hannun IRT.

Ahmed dan asalin garin Ibbi ne da ke jihar Taraba. Ya ce ya tabbatar da cewa Wadume ya shiga harkar garkuwa da mutane tun kafin jami'an tsaro su kama shi.

Dan shekaru 22 ya ce abokan Wadume da wani yayansa mai suna Awolu sun yi iyakar kokarinsu don samun sassauci ga shahararren mai garkuwa da mutanen.

Da gangan sojoji suka harbe jami'an IRT don ceton Wadume - Shaida
Da gangan sojoji suka harbe jami'an IRT don ceton Wadume - Shaida Hoto: Punch
Asali: UGC

A wata takarda da Ahmed yasa hannu a ranar 22 ga watan Augusta a garin Abuja, ya bayyana cewa kamen Wadume ya biyo bayan garkuwa da manyan masu kudi da kuma 'yan siyasa da ya fara yi.

Ya ce, "Ni makwabcin Wadume ne a Ibbi. Na san yana aiki da karamar hukuma kuma yana kasuwancin siyar da kifi. An kama ni saboda ina kokarin shawo kan matsalar Hamisu.

"Ya bani babur shiyasa nake kokarin shawo kan matsalarsa.

"Na san cewa sojoji ne suka kashe 'yan sanda don samun kubutar da Hamisu. Ban taba shiga tawagarsa ta garkuwa da mutane ba kuma bai taba bani kudi ba."

Wadume ya bayyana mutum 16 wadanda suke hada kai don garkuwa da mutanen. Ciki akwai Balarabe da wasu sojoji tara duk a tawagarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matsala ya kunno kai a PDP yayinda Wike ya zame daga lamarin zaben gwamnan Edo

Duk da bincike ya nuna akwai hannun sojin a ciki, hukumomin tsaro sun ki mika dakarun don fuskantar hukunci.

Antoni janar kuma ministan shari'a, Abubakar Malami, ya janye zargi 16 da yake yi ga balataliya ta 93 da ke Takum a jihar Taraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel