Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina

Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina

Tsohon shugaban hukumar gyaran harkar fansho, Abdulrasheed Maina, ya ce mamba mai wakiltar mazabar jihar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, ya amince zai tsaya masa a matsayin wanda zai karbi belinsa a hannun kotu.

Maina, wanda ke fuskantar tuhumar cin hanci a gaban kotu, ya bayyana hakan ne ta bakin lauyansa, Joe Kyari Gadzama (SAN), yayin zaman kotu na ranar Talata.

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ce ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa zarginsa da wawure wasu makudan kudade mallakar hukumar fansho.

Sanata Ndume bai halarci zaman kotun na ranar Talata ba, amma ma'aikatan gidan gyaran hali sun kawo Maina duk da ya na dogarawa da sandunan karfe.

Tun a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2019, kotu ta bayar da belin Maina, amma rashin cika sharudan bayar da shi beli suka sa aka cigaba da tsare shi a kurkuku kafin daga bisani lauyoyinsa su roki a sassauta sharudan belin.

Sanatan APC daga arewa ya amince zai karbi belin Maina
Yayin kawo Maina kotu a baya
Asali: UGC

Alkalin kotun, Jastis Okon Abang, ya amsa da rokon lauyoyin inda ya rage yawan sanatoci da zasu karbi belin Maina zuwa guda daya yayin wani zamana kotu a ranar 28 ga watan Janairu, 2020.

DUBA WANNAN: ICPC ta bankado badakalar miliyan N250 a asibitin UDUTH da ke Sokoto

Kazalika, ya rage adadin kudin belin Maina daga biliyan daya zuwa miliyan N500.

Sauran sharudan bayar da belin Maina sun hada da mallakar kadara da kudinta bai gaza miliyan N500 ba a unguwar Asokoro, Maitama, Wuse II, da wasu sassan birnin Abuja.

Tilas duk Sanatan da ya karbi belinsa ya ke raka shi kotu duk lokacin da za a zauna.

A yayin da aka koma zaman kotun ranar Talata, Gadzama ya sanar da alkalin kotun cewa Sanata Ndume ya amince zai tsayawa Maina domin karbar belinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel