Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Ondo yayinda ake shirin tsige mataimakin gwamna

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Ondo yayinda ake shirin tsige mataimakin gwamna

Rikicin da ke tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu da mataimakinsa, Agboola Ajayi, ya dauki sabon salo a safiyar ranar Talata, 23 ga watan Yuni, lokacin da jami’an yan sanda suka yi wa harabar majalisar dokokin jihar tsinke domin ba da kariya ga yan majalisa da ke shirin tsige Ajayi.

Mataimakin gwamnan na Ondo a ranar Lahadi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), inda hakan ya tada kura a kewaye da siyasar jihar.

Wata majiya a majalisar dokokin, wacce ta tabbatar da lamarin ga majiyarmu ta Sahara Reporters, ta ce a yanzu haka ma’aikata a majalisar na neman mafaka domin tsiratar da kansu.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Ondo yayinda ake shirin tsige matainakin gwamna
Yanzu Yanzu: Yan sanda sun mamaye majalisar dokokin Ondo yayinda ake shirin tsige matainakin gwamna Hoto: The Guardian
Asali: UGC

“Mun wayi gari mun ga jami’an yan sanda a harabar majalisar da safen nan suna tsatsaye a wasu wurare. Na jiyo daya daga cikinsu na fadin cewa kwamishinan yan sanda ne ya bukaci su tsaya a wajen.

KU KARANTA KUMA: Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Kaduna

“Akwai wani shiri na tsige mataimakin gwamnan tun bayan da ya sauya sheka zuwa PDP a ranar Lahadi kuma kasancewar yan sanda a wajen shine domin ba wasu yan majalisa masu biyayya ga gwamnan kariya don aiwatar da aikinsu.

“Na yi nasarar ficewa daga harabar yayinda sauran ma’aikata ke tserewa domin kada abun ya shafe su.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa sauya shekar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi zuwa jam'iyyar PDP ya sa wasu daga cikin manema tikitin jam'iyyar don takara ke korafi a kan yadda ake bai wa masu sauya sheka fifiko a jam'iyyar.

A kalla 'yan takara takwas ne suka siya fam don nuna ra'ayin fitowa takara, ciki kuwa har da Eyitayo Jegede (SAN).

Majiya mai karfi ta ce 'yan takarar na zargin mataimakin gwamnan da nada shugaban kwamiti tare da mambobin kwamitin zaben fidda gwani a jihar.

Wata majiya ta ce Ajayi da kansa ya biya wani jirgi guda don dauko kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP wanda ya samu jagorancin Prince Uche Secondus don karbarsa zuwa jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel