Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Kaduna

Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Kaduna

- Rundunar sojin sama ta dakile harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Kwauya-Tsamiya da ke jihar Kaduna

- Dakarun sojin sun kuma yi nasarar kwato shanun da yan ta'addan suka sace

- Sai dai kuma ba a rasa ran kowa ba illa wasu yan bindiga da suka tsere da raunika

Dakarun sojin saman Najeriya sun dakile harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Kwauya-Tsamiya da ke jihar Kaduna.

Kamar yadda takardar da ta fita a ranar Litinin daga hannun shugaban fannin yada labarai, Manjo Janar John Enenche, ya ce jami'an rundunar ta 404 da ta dakarun sojin saman sun dakile harin 'yan ta'adda da suka kai a sa'o'in farko na ranar Lahadi.

Manjo Janar Enenche ya yi bayanin cewa "rahotannin sun nuna cewa wasu masu satar shanu sun kai hari wata rugar Fulani tare da kwace Shanu ta hanyar amfani da bindiga."

Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Kaduna
Dakarun sojin sama sun dakile harin 'yan bindiga a Kaduna Hoto: The Sun
Asali: UGC

Runduna ta musamman na dakarun ne suka bi su inda suka kwato shanun da aka sace, Channels Television ta ruwaito.

"Rundunar wacce ta samu taimakon dakarun Operation BADAMAMAKI tare da hadin guiwar wasu 'yan banga, sun gaggauta gano inda 'yan bindigar suke sannan suka yi musu ruwan wuta.

"Hakan ne yasa suka watse tare da barin shanun," takardar tace.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatinka ce mafi muni a tarihin Najeriya – Tsohon minista Dalung ya caccaki Buhari

"A yayin da ba a rasa rai ko daya ba daga farar hular har zuwa dakarun sojin saman, wasu 'yan bindigar sun tsere da raunika.

"Hakan yasa aka jinjinawa kwazon dakarun tare da yin kira garesu da su kara dagewa wurin shawo kan matsalar 'yan bindiga da duk wani nau'in rashin tsaro da ya zama babban kalubale ga zaman lafiyar kasar nan."

A gefe guda, mun ji a baya cewa daya daga cikin 'yan bindiga ya rasa ransa yayin da wasu da yawa suka samu raunika yayin da dakarun soji suka kai samame maboyarsu da ke jihar Binuwai.

Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar tsaro, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce an kai samamen a ranar Asabar kuma dakarun sun yi nasarar tarwatsa maboyar 'yan bindigar tare da samun makamai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel