ECOWAS za ta marawa Ngozi Okonjo-Iweala baya a takarar Kungiyar WTO

ECOWAS za ta marawa Ngozi Okonjo-Iweala baya a takarar Kungiyar WTO

- Kungiyar ECOWAS ta na goyon bayan takarar Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a WTO

- Kasashen Yammacin Afrika za su marawa tsohuwar Ministar Najeriya baya

- ‘Yar takarar Najeriyan ta na fuskantar adawa a zaben WTO daga kungiyar AU

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust cewa kungiyar ECOWS ta Kasashen yammacin Afrika za su marawa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala baya wajen takarar kujerar kungiyar WTO.

Shugabannin kasashen ECOWAS sun yi wa takarar Ngozi Okonjo-Iweala mubaya’a a zaben da za ayi. Ngozi Okonjo-Iweala ta na neman kujerar Darekta janar na wannan kungiya.

Idan Okonjo-Iweala ta yi nasarar lashe zaben da za ayi, za ta jagoranci kungiyar kasuwancin Duniya na tsawon shekaru hudu, wanda wa’adinta zai fara daga 2021 zuwa 2025.

Daga lokacin da aka kafa kungiyar WTO a watan Junairun 1995 zuwa yanzu, ba a taba samun 'Dan Afrika da ya rike kungiyar ba, idan an yi dace wannan karo za a karya lagon.

KU KARANTA: WTO ta yarda Ngozi Okonjo-Iweala ta yi takarar Darekta a zaben 2020

ECOWAS za ta marawa Ngozi Okonjo-Iweala baya a takarar Kungiyar WTO
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala
Asali: Twitter

Ferdinand Nwonye ya bayyana cewa shugabannin ECOWAS na kasashen Afrika ta yamma da gwamnatocin kasashen su na goyon bayan Okonjo-Iweala saboda kwarewar aikinta.

Daga cikin dalilan ECOWAS na goyon bayan Okonjo-Iweala akwai: “Dadewa a aiki a manyan hukumomi, kaurin-suna na kawo gyara, da kwarewa a yarjejeniya da sanin siyasa.”

Nwonye ya ce tsohuwar Ministar Najeriyar, “Ta shafe shekaru fiye da 30 a matsayin masaniyar cigaban tattalin arziki, wanda ta san harkar kasuwanci, kuma ta ke da ilmin tattali.”

“Ta rike Darekta a babban bankin Duniya, kuma yanzu ita ce shugabar majalisar da ke sa ido a GAVI, kuma jakadar AU ta musamman wajen tara gudumuwar yaki da COVID-19.”

Najeriya ta samu goyon bayan kungiyar ECOWAS ne jim kadan bayan kasar Benin ta fito ta janye ‘dan takararta. Makwabciyar Najeriya, Benin ta ce za ta ba Okonjo-Iweala kuri’arta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel