Masu harkar mai sun fara yi wa Minista barazanar tafiya yajin aiki saboda maganar IPPIS

Masu harkar mai sun fara yi wa Minista barazanar tafiya yajin aiki saboda maganar IPPIS

Najeriya na iya fuskantar wahalar man fetur idan har ma’aikata su ka shiga yajin aiki a fadin kasar a dalilin yunkurin da ake neman yin a jefa su a karkashin tsarin biyan albashi na IPPIS.

Rahotanni daga jaridar Punch sun bayyana cewa ma’aikatan mai su na barazanar yin yaji, muddin gwamnatin tarayya ta hakikance a kan maida su cikin manhajar IPPIS na biyan albashi.

Kungiyoyin NUPENG da PENGASSAN na manyan ma’aikatan mai da masu jigila sun rubutawa karamin ministan harkokin man fetur, Timipre Sylva, wasikar barazanar janye aiki a fadin kasar.

A wannan wasika da ta fito daga NUPENG da PENGASSAN, ma’aikatan sun nuna rashin goyon bayansu ga yunkurin da babban Akawun gwamnatin tarayya ya ke yi na sa su cikin IPPIS.

Ma’aikatan sun shaidawa Timipre Sylva cewa bai dace a jefa ma’aikatan mai a wannan manhaja na IPPIS ba domin su na da wasu bambance-bambance na musamman a game da albashinsu.

KU KARANTA: Litar Fetur ya koma N121 a Najeriya

Masu harkar mai sun fara yi wa Minista barazanar tafiya yajin aiki saboda maganar IPPIS
Kungiyar NUPENG da Shugaban kasa Hoto: Aso Villa
Asali: Depositphotos

Sakatarorin wadannan kungiyoyi biyu; Lumumgba Okugbawa da Olawale Afolabi ne su ka sa hannu a wasikar. An rubuta wannan takarda ne tun a ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni, 2020.

NUPENG da PENGASSAN sun bukaci a zauna a tebur a shawo kan lamarin albashin ‘ya ‘yansu. Shugabannin kungiyoyin sun nemi gwamnati ta tuntubi shawararsu kafin ta zartar da hukunci.

“Mu na jaddada cewa babu tabbacin samun zaman lafiya a wurin aiki idan aka dakatar da albashin mutanenmu, ko kuma aka dabbaka (tsarin IPPIS) ba tare da mun kawo ta-cewa ba”

Olawale Afolabi ya shaidawa jaridar a ranar Litinin cewa ma’aikatan mai za su tafi yajin aiki, muddin gwamnati ta yi watsi da bukatarsu. Sai dai Afolabi bai fadi lokacin da zasu janye aiki ba.

Afolabi da takwarorinsa sun yi tarayya da kungiyar ASUU wajen zargin manhajar ASUU da kawo matsala, su ka nemi a sake tunanin yin abin da zai jawo a fara wahalar man fetur a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel