Lionel Messi da Antoine Griezmann sun samu sabani a wajen atisaye
- Lionel Messi bai ji dadin canjaras din da Barcelona ta yi da Sevilla ba
- Babban ‘Dan wasan ya samu kansa a sabani da Antoine Griezmann
- Ana rade-radin sai da Koci Quique Setien ya shiga tsakanin ‘Yan wasan
Rahotanni sun bayyana cewa an samu fada tsakanin manyan ‘yan wasan gaban kungiyar kwallon kafan Barcelona Lionel Messi da kuma Antoine Griezmann.
Taurarin sun kaure da fada a wurin atisaye a farkon makon nan. Ana tunanin cewa ‘yan kwallon sun samu matsala ne a sakamakon wasan Sevilla na Ranar Juma’a.
Lamarin har ya kai sai da mai horas da ‘yan wasan Barcelona Quique Setien ya zo ya raba ‘yan kwallon na sa da aka dade ana rade-radin cewa ba su jituwa sosai.
A wasan da Barcelona ta buga da kungiyar Sevilla, an tashi canjaras, babu wanda ya yi nasara. Wannan ya taimakawa Real Madrid wajen darewa samun tebur.
KU KARANTA: Wasu 'Yan wasan Barcelona sun kamu da COVID-19
Jaridar Diario Gol ta kasar Sifen ta ce rikicin Messi da Griezmann ya fara bayyana karara, wanda hakan ya jawo sai da Koci Setien da wasu ‘yan wasa su ka raba su.
A wasan da Barcelona ta buga da kungiyar Leganes, har aka tashi Lionel Messi bai ba Griezmann kwallo a cikin minti 90 da aka buga ba, a karshe Barcelona ta ci 2-0.
A kakar shekarar bara ne Barcelona ta saye ‘dan wasan gaba Griezmann mai shekara 29 da haihuwa daga kungiyar Atletico Madrid a kan fam miliyan £108.
A halin yanzu Griezmann ya zurawa Barcelona kwallaye 14, sannan kuma ya yi sanadiyyar cin kwallaye hudu, inda ake neman Messi ya sa hannu a sabon kwantiragi.
Ana jita-jitar kungiyar Barcelona ta fara tunanin saida ‘dan wasan kasar Faransar bayan ya gaza samun zaman lafiya da babban Tauraron Duniya watau Lionel Messi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng