Abinda yasa muka ziyarci Buhari - Shugaban gwamnonin APC, Bagudu
A ranar Litinin ne kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) ta ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa domin sanar da shi matsayar mambobin kungiyar dangane da rigingimun da jam'iyyar APC ke fama da su a kasa.
Shugaban PGF kuma gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu, ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala ganawarsu da shugaba Buhari a fadarsa, Villa, da ke Abuja.
Bagudu ya bayyana cewa suna goyon bayan shugaba Buhari domin ya kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a bullowa rigingimun shugabanci da suka dabaibaye jam'iyyar APC.
Gwamnan na jihar Kebbi ya na tare da takwarorinsa na jihar Filato; Simon Lalong, da na jihar Jigawa; Abubakar Badaru, yayin da ya ke wannan jawabi.
A cewar Bagudu, shugaba Buhari ya bawa gwamnonin tabbacin samun goyon bayansa a dukkan matakin da zasu dauka na dawo da zaman lafiya a cikin jam'iyyar APC.
Ya kara da cewa, duk da shugaba Buhari ba zai cusa wani mutum a wata kujerar shugabancin jam'iyya ba, ya nuna niyyarsa na dukan matakan da zasu kwantar da kurar da ta tashi a cikin gidan APC.
DUBA WANNAN: Abinda yasa gwamnatin Buhari ta batawa Trump rai - Tsohon mai bashi shawara a kan tsaro
"Mun ziyarce shi domin tattauna matsalolin da jam'iyyarmu ta ke ciki a matsayinsa na shugaban da miliyoyin 'yan Najeriya suka yarda da shi.
"Mu tattauna batutuwan da suka shafi jam'iyya da kuma hada karfi da karfe wajen daukan matakan da zasu dinke barakar da ta kunno kai a cikin jam'iyyar APC.
"Shugaban kasa ya sauraremu da kunnen basira, kamar yadda uba zai saurari 'ya'yansa, kuma ya bamu tabbacin da muke bukata a kan cewa nan bada dadewa ba za a warware dukkan matsalolin da jam'iyyar APC ke fama da su," a cewarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng