Sanata Usman Kadiri ya lissafa mutane biyu da ke barazanar rusa APC

Sanata Usman Kadiri ya lissafa mutane biyu da ke barazanar rusa APC

Tsohon mamba a majalisar dattijai daga jihar Kwara, Sanata Dakta Alex Usman Kadiri, ya ce Ahmed Bola Tinubu da Kwamred Adams Oshiomhole sune babbar barazanar da jam'iyyar APC ke fuskanta a Najeriya.

Yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja, tsohon dan majalisar ya bayyana cewa Tinubu ne ya yi cushen Oshiomhole har ya zama shugaban jam'iyyar APC saboda biyan bukatarsa na son yin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Kadiri ya bayyana mamakinsa a kan yadda jam'iyyar APC za ta mika takarar shugaban kasa ga Tinubu a shekarar 2023 idan har yankin kudu maso yamma ne zai fitar da dan takara.

A cewar Kadiri, kuskure ne da rashin dacewa a saka Tinubu a gaba daga yankin kudu maso yamma bayan akwai mutane masu kima da daraja daga yankin irinsu mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

"Ni ba na sha'awar salon siyasar Tinubu. Tun asali ya kafa Oshiomhole ne saboda burinsa na son yin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

"Idan har APC za ta mika takarar shugaban kasa zuwa yankin kudu maso yamma, me yasa ba zata yi tunanin bawa mutum mai basira kamar Osinbajo ba, me yasa za a yi tunanin dauko wani Tinubu?," a cewar sanata Kadiri.

Da ya ke magana a kan jimurdar da ke tsakanin Oshiomhole da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, sanata Kadiri ya bayyana abinda ya ke faruwa da Oshiomhole a matsayin 'kaikayi koma kan mashekiya'.

Sanata Usman Kadiri ya lissafa mutane biyu da ke barazanar rusa APC
Oshiomhole da Tinubu
Asali: UGC

Sanata Kadiri ya ce kafin Oshiomhole ya bar ofishin gwamna sai da ya zagi duk wasu manyan mutane masu kima da ke jihar Edo tare da tsinewa siyasar ubangida, amma kuma daga karshe ya na saka ran ya zama ubangidan gwamna Obaseki.

DUBA WANNAN: Gwamnatin Kano ta haramta goyo a babur, ta bayyana dalili

"Idan da ranka za ka sha kallo; sai da Oshiomole ya zagi duk wasu manyan mutane masu daraja da kima da ke jihar Edo, ya tsinewa siyasar ubangida, ya kira mutumin da yake goyawa baya a yanzu, Ize Iyamu, da barawo.

"Ya zagi manyan mutane irinsu Toni Anini, ya zagi babban sarki Igbinedion, ya zargi dansa; Lucky Igbinedion, tsohon gwamna, ya ce dukkansu barayi ne. Amma, yanzu so yake ya zama ubangidan gwamna, sai yadda ya juya shi," a cewarsa.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa burin Tinubu da son ran Oshiomohole zasu iya durkusar da jam'iyyar APC matukar ba a dauki wani mataki domin gyaran al'amura kafin su gama tabarbarewa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel