Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki

Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki

A ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi magana a kan rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar APC mai mulki.

Lawan ya yi zancen ne bayan ganawarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa.

"A gaskiya sai mun shawo kan matsalar da muke fama da ita a jam'iyya mai mulki. Mu ke da shugaban kasa, mafi yawan sanatoci da kuma gwamnonin mafi yawa a kan kowacce jam'iyyar siyasa."

An fara rikicin shugabancin jam'iyyar ne bayan kotun daukaka kara ta dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole inda ta jaddada hukuncin babban kotun tarayya.

Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki
Rikicin APC: Shugaban majalisa, Ahmed Lawan ya saka baki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jam'iyyar ta bayyana Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo da ya bayyana a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar tunda shine mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.

Amma tsohon mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa, Victor Giadom ya bayyana kansa a matsayin mukaddashin shugaban dogaro da umarnin da wata kotu ta bada a watan Maris a lokacin da aka fara dakatar da Oshiomhole.

Jam'iyyar ta yi dogaro da kundun tsarin mulkinta inda ta bayyana cewa babu kowa a kan kujerar Giadom saboda da kansa yayi murabus a 2018.

Tuni bangaren jam'iyyar na jihar Ribas ta zabi wani madadin Giadom din tare da dakatar da shi a jihar.

Bugu da kari, jam'iyyar APC ta jihar Ribas ta samu hukuncin kotu a ranar Alhamis inda ta haramta wa Giadom bayyana kansa a matsayin mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa.

Lawan ya sanar da manema labarai cewa ba za a bar wannan al'amarin ya hargitsa APC ba don daidaituwar na daidai da daidaituwar Najeriya. Jam'iyyar ce ke juya akalar mulkin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume

"A gaskiya akwai bukatar mu daidaita komai ta yadda ayyukanmu za su yi kyau tare da sauki.

"Don haka jam'iyyar ce jigo kuma mai matukar amfani wurin tabbatar da cewa Najeriya na ci gaba."

Lawan ya kalubalanci shugabannin jam'iyyar na kasa da su yi namijin kokari wurin sasanta 'ya'yanta.

Ya jaddada cewa, "Da izinin Allah nan da kwanaki kadan za mu ga an dauki mataki kuma akwai fatan dukkan shugabannin jam'iyyar a fadin kasar nan za su saka baki."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng