Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume

Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, wanda yanzu shine shugaban kwamitin kula da sojin kasar nan, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa 'yan majalisar tarayya da masu manyan mukamai a kasar nan ne ke morar albashi mai tarin yawa.

Sai dai kuma ya ce talakawan Najeriya ke cikin wani hali, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi sun yi gaskiya a kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya cike da tsada wanda yace ba dole bane hakan ya ci gaba.

Ndume ya sanar da hakan ne yayin martani ga Osinbajo da Sanusi yayin tattaunawa a kan daidatuwar tattalin arziki bayan annobar korona.

A yayin da aka tattauna da Sanusi, ya bayyana cewa tsarin da ake bi na tafiyar da gwamnati a Najeriya na nuna cewa za ta durkushe kuma ya tambayi mataimakin shugaban kasa a kan abinda gwamnatin nan ke yi don shawo kalubalen.

Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume
Hankalinmu ba zai kwanta ba saboda talaka bashi da walwala - Sanata Ndume
Asali: Twitter

A martanin Osinbajo, ya ce "Ba sai an tambaya ba, an san muna ma'amala da gwamnati mai girma kuma a tsadance. Amma kuma kamar yadda kuka sani, wadanda za su saka kuri'a kan rage tsadar gwamnatin sune 'yan majalisar."

Ndume ya ce, "Kasafin kudinmu na tiriliyan 10 na nuna cewa kashi 30 daga ciki ne za a mika ga manyan ayyuka, kashi 70 zai tafi ne ga kanana. Wannan tsarin sam bai dace ba.

"A wannan tsarin, ana biyan ma'aikata da albashin da zai ishesu rayuwa kawai, kadan daga cikinsu ne suke samun rayuwa mai walwala. 'Yan majalisar dattawa har da ni a ciki, mu ake biya albashin da muke watayawa a ciki.

"Ta yaya hankali zai kwanta bayan kadan daga cikinmu ne ke jin dadi babu talauci tare da mu? Karancin albashin N30,000 yayi kankanta. Dole ya sa ma'aikata su fada harkar rashawa don tsira."

KU KARANTA KUMA: A karon farko: Gwamnan Bauchi ya yi martani a kan zargin damfara da ICPC ke masa

Sanatan mai wakiltar mazabar jihar Borno ta tsakiya, ya jaddada cewa kudin da ake kashewa don tafiyar da gwamnati yayi yawa.

Ndume ya ce akwai bukatar sauya tsarin mulkin majalisar dattawa saboda tsarin yanzu su kadai yake wa dadi.

Ndume ya ce, "Akwai bukatar kawo sauyi a tsarin mulki ta yadda za a mayar da shugabannin daidai da ma'aikata.

"Hakazalika, ana iya zabar ministoci daga cikin 'yan majalisar da aka zaba. Wannan zai sa a rage yawan kudin da shugabanni ke karba sannan ya kawo mulki mai inganci."

Ndume ya ce akwai bukatar masana shari'a su hada kai don tsara yadda za a sauya kundun tsarin mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel