Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa motar shugaban NDDC ruwan harsasai

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa motar shugaban NDDC ruwan harsasai

- Tsohon shugaban ayyuka na hukumar NDDC, Injiniya Samuel Adjogbe a daren Asabar ya tsallake rijiya da baya

- Hakan ya biyo bayan hari da wasu yan bindiga suka kai wa motarsa a yankin Ughelli, Evwreni na Ogor a titin gabas maso yamma na jihar Delta

- Sai dai babu abunda ya same shi amma an harbi direbansa a kai

Tsohon darakatan ayyuka na hukumar kula da ci gaban a yankin Niger Delta (NDDC), Injiniya Samuel Adjogbe a daren Asabar ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin 'yan bindiga.

Ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar The Nation ta hirar wayar tafi-da-gidanka.

Ya yi bayanin cewa sun kai masa hari ne a yankin Ughelli, Evwreni na Ogor a titin gabas maso yamma na jihar Delta.

Adjogbe ya yi bayanin cewa an yi mishi ruwan harsasai a kan motarsa kirar Lexus 570, musamman a saitin mazaunin mai motar amma sai yayi sa'a ba a samesa ba.

Amma kuma an harbi daya daga cikin wadanda ke cikin motar mai suna Samuel Adibor a kai.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa motar shugaban NDDC ruwan harsasai
Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi wa motar shugaban NDDC ruwan harsasai Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya ce a halin yanzu Adibor yana asibiti inda yake karbar taimakon masana kiwon lafiya a Ughelli kuma sun kai rahoto ofishin 'yan sanda.

Ya ce: "An kai mana hari tsakanin Ughelli da Evwreni a kan hanyarmu ta zuwa Ughelli da misalin karfe 7:40 na yamma. An harbi direbana mai suna Samuel Adibor a kansa.

"A halin yanzu yana karbar taimako a wani asibiti a Ughelli. Nagode Ubangiji da babu rashin rai da aka yi."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mataimakin gwamnan jihar Ondo ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Wata majiya daga ofishin 'yan sandan yankin ta tabbatar da aukuwar lamarin amma 'yan sanda na kan al'amarin.

A wani labari na daban, mun ji cewa akalla daya daga cikin 'yan bindiga ne ya rasa ransa yayin da wasu da yawa suka samu raunika yayin da dakarun soji suka kai samame maboyarsu da ke jihar Binuwai.

Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar tsaro, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Lahadi.

Ya ce an kai samamen a ranar Asabar kuma dakarun sun yi nasarar tarwatsa maboyar 'yan bindigar tare da samun makamai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel