Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa

Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, ta ce rahotannin kwace kadarar gwamnan Bala Mohammed ta miliyoyin naira da ICPC tayi ya isa ya zama hujjar da za ta sa ya yi murabus a matsayin gwamnan jihar ko a tsigesa.

Idan za mu tuna, an kwace kadararsa ta Zinaria International School wacce ke fuloti na 298 da ke yankin Wuye, Cadastral Zone B3 a birnin tarayya.

A yayin tabbatar da kwace ginin, kakakin hukumar ICPC, Rasheedat Okoduwa ta ce ba za su iya gurfanar da Mohammed ba saboda kariyar da yake da ita kamar yadda sashi na 308 na kundun tsarin mulki ya bayyana.

Hukumar ta sanar da cewa za ta gurfanar da gwamnan ne bayan ya kare wa'adin mulkinsa.

Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa
Zargin damfara: APC ta bukaci gwamnan Bauchi ya yi murabus ko a tsigesa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Amma jam'iyyar APC ta yi kira ga gwamnan da ya sauka daga mulkin jihar a mutunce.

Wannan bukatar na kunshe ne a wata takarda da jaridar The Nation ta samu bayan shugaban kwamitin yada labarai na jam'iyyar APC a jihar, Kwamared Sabo Mohammed da sakatare Mallam Sa'adu Umar suka sa hannu.

"APC ta gano handamar da gwamna Bala Mohammed yayi na wata kadara wacce ICPC ta kwace a Abuja.

"Kakakin hukumar ICPC ta ce Gwamna Bala Mohammed ya samu dukiyar ne ba ta yadda ya dace ba kuma mallakin ma'aikatar noma da kiwo ce.

"Wannan wawurar za ta iya bada damar ya sauka daga mulki ko a tsigesa. A don haka muke kira gareshi da ya bi hanyar da ta dace a mutunce," takardar tace.

Amma a martanin gaggawa da gidan gwamnatin jihar ya fitar, ya musanta rahoton hukumar wanda ta ce labaran kanzon kurege hukumar ke fadi a kan gwamnan.

A baya mun ji cewa hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) a ranar Talata, 16 ga watan Yuni, ta sanar da kwace wani gini mallakin Sanata Bala Muhammad wanda ya same shi a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya Abuja.

Ginin ne Zinaria International School da ke fuloti 298, yankin Wuye, Cadastral Zone B3 Abuja.

Kamar yadda takardar ta bayyana a shafin hukumar ta Twitter, ta ce bincike ya nuna cewa Sanata Mohammed ya mika ginin makarantar ga hukumar a lokacin da yake ministan babban birnin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel