Benue: Sojoji sun ragargaza 'yan bindiga a maboyarsu, daya ya rasa ransa

Benue: Sojoji sun ragargaza 'yan bindiga a maboyarsu, daya ya rasa ransa

A kalla daya daga cikin 'yan bindiga ne ya rasa ransa yayin da wasu da yawa suka samu raunika bayan da dakarun soji suka kai samame maboyarsu da ke jihar Binuwai.

Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar tsaro, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya bai wa manema labarai a ranar Lahadi, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce an kai samamen a ranar Asabar kuma dakarun sun yi nasarar tarwatsa maboyar 'yan bindigar tare da samun makamai.

Benue: Sojoji sun ragargaza 'yan bindiga a maboyarsu, daya ya rasa ransa
Benue: Sojoji sun ragargaza 'yan bindiga a maboyarsu, daya ya rasa ransa Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Takardar ta ce, "Rundunar Operation Whirl Stroke karkashin Operation Accord sun samu rahoton al'amuran 'yan bindiga a yankin Ginda da ke Saghev a karamar hukumar Guma ta jihar Binuwai.

"Dakarun sun kai samame a ranar 20 ga watan Yunin 2020 inda suka tarwatsa maboyar 'yan bindigar.

"Tuni 'yan bindigar suka tsere inda a nan aka halaka daya daga ciki yayin da wasunsu suka tsere da raunika sakamakon harbin bindiga.

"Abubuwan da aka samu a wurinsu sun hada da harsasai, bindigogi, babur daya, kayan soja, wiwi da kuma layu. An tarwatsa sansanin daga bisani."

A wani ci gaba, sojojin sun kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da wani malami a jihar Binuwai.

KU KARANTA KUMA: Wasu gwamnonin APC na goyon bayana - Obaseki

Takardar tace, "Dakarun soji da ke Tunga sun yi martani tare da daukar mataki a kan garkuwa da wani malami da aka yi a karamar hukumar Foga.

"Sun damke mutane biyu da ake zargi. Akwai Yahuza Danlami da Danladi Baushe da ake zargin suna da hannu a ciki.

"An samu bindigar toka a tare da su. Tuni aka mika wadanda ake zargin zuwa hannun rundunar 'yan sandan Najeriya da ke Awe don bincike.

"Hedkwatar tsaron ta jinjinawa dakarun a kan kokarinsu na yaki da 'yan bindigar tare da dukkan wani ta'addanci."

A wani labarin kuma, mun ji cewa Mambobin kungiyar gwamnonin arewa sun yi taro a ranar Alhamis don duba yanayin rashin tsaro da ya addabi yankin.

Taron da aka yi ta yanar gizo wanda shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong, ya jagoranta, ya jajanta a kan karuwar rashin tsaro a yankunan arewa.

A yayin taron, gwamnonin sun fara zantawa a kan matakan dauka a kan rashin tsaron.

Daga cikin matakan, sun amince da kafa kwamitin kula da tsaro a arewa wanda zai dinga duba al'amuran tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, shi aka nada shugaban kwamitin yayin da Gwamna Matawalle na jihar Zamfara da takwaransa na Gombe, Muhammad Yahaya suka zama mambobi.

Daya kwamitin ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamna Ahmadu Fintiri, Abubakar Bello da Aminu Tambuwal.

Sunce za su tuntubi malaman addinai, sarakunan gargajiya da shugabannin yankuna a arewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel