Wasu ‘Daliban Edo, A/Ibom, Ogun Anambra, Delta, da Ekiti sun fi kowa samun nasara a UTME – JAMB
Hukumar nan JAMB da ke shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare a kasa ta bayyana jihohin da hazikan yaran da su ka yi fice a jarrabawar wannan shekara su ka fito.
Yara 13 ne aka samu a sahun goma na farko da su ka samu gagarumar nasara a jarrabawar UTME a bana. Wadannan yara ne su ka fi kowa lashe jarrabawar da aka yi kwanakin baya.
Jaridar Punch ta ce duka wadannan hazikai sun yi tarayya wajen sha’awar su karanci ilmomin fasaha a jami’o’in Najeriya. Haka zalika dukkansu sun fito ne daga yankin Kudancin kasar.
Wadannan yara sun fito ne daga jihohin Anambra, Edo, Delta, Ekiti, Ondo, Akwa Ibom, Kwara, Oyo, da kuma jihar Ogun. Jihar Kwara da ke Arewa ta tsakiya ce ta ceci kaf jihohin da ke Arewa.
Daga cikin yaran nan da su ka samu nasara a jarrabawar UTME, biyar sun cike jami’ar Legas ne, biyu daga cikinsu su na da burin su yi karatu a jami’ar kudi ta Covenant da ke jihar Ogun.
Rahoton ya ce akwai yara biyu da su ka zabi su yi karatun digirinsu a jami’ar Obafemi Awolowo, wasu biyu su na neman shiga jami’ar Ilorin. Sauran sun cike jami’ar Kwara da ta Ibadan.
KU KARANTA: 'Yan Sanda sun fito da Matashin da aka kama ya shirya zanga-zanga
Maduafokwa Egoagwuagwu Agnes wanda ya fito daga jihar Anambra shi ne wanda ya fi kowa samun maki a jarrabawar bana inda ya ci 365 a cikin 400.
Na biyu shi ne Nwobi Okwuchukwu David mai maki 363. Shi ma wannan ya fito ne daga Anambra.
Ojuba Mezisashe Shalom da Elikwu Victor Chukwuemeka daga Edo da Delta sun samu maki 359. Wanda ya ci 358 shi ne Adebola Oluwatobi Paul daga jihar Ekiti a Kudu maso yammacin kasar.
Gboyega Oluwatobiloba Enoch da ya fito daga jihar Ekiti shi ne ya zo na shida.
Ojo Samuel Oluwatobi da Utulu Jebose George daga jihar Ondo sun samu maki 355. Osom Akan Awesome ya zo na tara da maki 353, Awesome ya fito ne daga Akwa Ibom.
Yara hudu su ka rufe sahun farko da maki 352; Akakabota Fejiro Simeon daga Delta, Ogundele Favour Jesupemi daga Kwara, Alatise Monsura Bisola daga Oyo sai kuma Adelaja Oluwasemilore Daniel daga Ogun.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng