Rikicin APC babban kalubale ne ga ginin da ka fara - Lukman ga Buhari

Rikicin APC babban kalubale ne ga ginin da ka fara - Lukman ga Buhari

Darakta janar na kungiyar gwamnonin APC, Salihu Lukman, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki mataki a kan rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar APC.

Wannan na kunshe a wata takarda da ta fito daga darakta janar din PGF wacce aka bai wa manema labarai a garin Abuja a ranar Alhamis.

Lukman ya ce, "Abin takaici game da al'amarin shine yadda Buhari ya nuna bai damu ba bayan ya san hakan zai iya bata masa suna.

"Abun farin ciki shine yadda salon mulkinsa ke tabbatar da cewa jam'iyyar za ta iya zaman kanta. Amma kuma hakan na iya hana jam'iyyar cimma manufarta gaba da 2023."

Kamar yadda yace, duk wani dan jam'iyyar APC dole ya ji kunyar abinda ke faruwa da shugabannin ta wanda ya ce "a hankali take daidaicewa sakamakon nakasar shugabannin ta."

Rikicin APC babban kalubale ne ga ginin da ka fara - Lukman ga Buhari
Rikicin APC babban kalubale ne ga ginin da ka fara - Lukman ga Buhari Hoto: The Guardian
Asali: UGC

PGF kungiya ce ta dukkan gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar APC. A halin yanzu, akwai 'yan kungiyar 20 cif.

Lukman ya jaddada cewa yanzu lokaci ne da duk wani shugaba nagari na jam'iyyar da zai tashi tsaye ya fada a ji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: PDP ta daga ranar yin zaben fidda gwani a Edo

Yana mamakin yadda jam'iyyar siyasar da ke da shugabanni irinsu Manjo janar Muhammadu Buhari, Asiwaju Ahmed Tinubu, Bisi Akande, Sr Ogbonnayq Onu da sauransu ta kasa gyara cikin gidanta don cikar burin iyayen jam'iyyar.

Ya bukaci a hada taron shugabannin jam'iyyar na kasa inda za a shawo kan dukkan matsalolin.

A wani labarin kuma, Jam'iyyar APC mai mulki a ranar Alhamis ta rantsar da kwamitin zaben gwamnoni na jihar Edo da kuma na daukaka karar zaben fidda gwani da za a yi a ranar 22 ga watan Yuni don fitar dan ta kara a zaben da za a yi a watan Satumba.

Mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abiola Ajimobi, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa na yankin kudu-kudu, Hillard Etagbo Eta ya umarci kwamitin da su tabbatar da nasarar fitar da dan takarar gwamnan da ya cancanta.

Kwamitin mutum bakwai ya samu shugabancin Gwamnan jihar Imo, Hope Uzordinma da Sanata Ajibola Bashiru a matsayin sakatare.

Kwamitin daukaka karar zaben ya samu shugabancin Dr. Yusuf Nawai da Dr. Kayode Ajulo a matsayin sakatare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel