Kwamitin gudanarwa na APC ya saka mukamin Giadom a kasuwa

Kwamitin gudanarwa na APC ya saka mukamin Giadom a kasuwa

Kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar APC ya bayyana bukatar maye gurbin mataimakin sakataren jam'iyyar, Victor Giadom da wani.

Hakazalika, 16 daga cikin 'yan kwamitin gudanar da ayyukan jam'iyyar sun amince da Ajimobi a matsayin mukaddashin shugaban jam'iyyar na kasa.

Wadanda basu amince da Ajimobi ba a matsayin mukaddashin shugaban sun hada da mataimakin shugaban jam'iyya na Arewa, Lawal Shuaibu, Giadom da mataimakin shugaban jam'iyya na yankin arewa maso gabas, Mustapha Salihu.

Binciken da jaridar The Nation tayi ta gano cewa NWC sun yanke shawarar kwace kujerar Giadom ganin cewa tun daga 2018 ya daina shugabanci a jam'iyyar.

Kwamitin gudanarwa na APC ya saka mukamin Giadom a kasuwa
Kwamitin gudanarwa na APC ya saka mukamin Giadom a kasuwa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Giadom ya yi murabus a 2018 saboda tsayawar da zai yi a takarar mataimakin gwamnan jihar Ribas a karkashin jam'iyyar APC.

Amma bayan hana jam'iyyar APC fidda dan takara a 2019, Giadom ya koma ofishinsa da ke hedkwatar jam'iyyar ba tare da anyi sabon zabe ba a yankin kudu-maso kudu.

NWC ta ce dogaro da tanadin jam'iyyar, Giadom ya tashi daga matsayin shugaba a jam'iyyar tun a 2018.

An gano cewa, NWC ta bukaci yankin kudu maso kudu na jam'iyyar APC da ta sake gabatar da Giadom ko kuma ta gabatar da wani sabon dan takara don cike gurbin mataimakin sakataren jam'iyyar na kasa.

KU KARANTA KUMA: Bashin da ake bin Najeriya: Lai Mohammed ya yi wa Atiku martani mai zafi

Sakataren jam'iyyar wanda ya zanta da The Nation ya ce: "Idan aka dogara da sashi na 31 na kundun tsarin mulkin APC, Giadom ya bar kujerarsa tun a 2018 kafin ya fito takarar mataimakin gwamna.

"Dogaro da kundun tsarin mulki, NWC na bukatar mai maye gurbinsa kafin a yi sabon zaben shugabannin jam'iyyar.

"A taronmu, mun bayyana cewa yankin kudu maso kudu za ta iya sake zabar Giadom ko kuma ta kawo wani."

A wani labarin kuma, mun ji cewa an rufe majalisar jihar Edo na makonni biyu.

Mukaddashin daraktar majalisar, Stephen Guobadia ya sanar da hakan a wata takarda inda ya bukaci 'yan majalisar da su kauracewa zauren majalisar har sai an yi mishi feshi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng