Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello

Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello

- Hadimin Gwamna Yahaya Bello na musamman, Abdulateef Suleiman, ya rasu

- Gwamnatin jihar Kogi ce ta sanar da labarin mutuwarsa a ranar Laraba, 17 ga watan Yuni

- An kwantar da marigayin a wani asibitin kudi da ke Abuja kafin mutuwarsa

Hadimi na musamman ga Gwamna Yahaya Bello, Abdulateef Suleiman, ya rasu.

A wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Onogwu Muhammed a ranar Laraba, 17 ga watan Yuni, ya bayyana cewa marigayi Suleiman ya rasu a wani asibitin kudi da ke Abuja.

Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello
Gwamnatin Kogi ta sanar da mutuwar hadimin Gwamna Bello Hoto: The Sun
Asali: UGC

"Muna bakin cikin sanar da mutuwar hadimi na musamman ga gwamnan jihar Kogi, Abdulateef Suleiman.

“An kwantar da marigayin ne a wani asibitin kudi da ke Abuja domin jinya amma ya rasu sakamakon bugun zuciya a safiyar yau.

“Za'a binne shi a yau bisa ga koyarwar addinin Islama. Allah ya ji kansa,” in ji jawabin.

Legit.ng ta tattaro cewa marigayi Suleiman ya rasu yana da shekara 41.

KU KARANTA KUMA: Dakatar da Oshiomhole: Babbar kwanciyar hankali ta samu APC - Jigon APC

A wani labarin kuma, a kwanakin baya ne wani ma'aikacin gidan gwamnatin jihar Gombe ya rasu sakamakon annobar korona, lamarin da yasa aka rufe ofishin sakataren gwamnatin jihar tare da bada umarnin yin feshi a asibitin gidan.

Shuaibu Danlami darakta ne na ayyuka na musamman da siyasa a ofishin sakataren gwamnatin jihar kuma ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, kwamitin yaki da annobar korona ta jihar ta sanar.

An diba samfur dinsa wanda sakamakon ya bayyana cewa yana dauke da cutar korona.

Danlami mamba ne kuma mataimakin sakataren kwamitin yaki da cutar na jihar kuma an dauka samfur din dukkan 'yan kwamitin.

Jami’ai sun kuma yi kokarin zakulo wadanda suka yi mu'amala da mamacin. An yi kokarin zakulo su ne domin yi musu gwaji da kuma killace duk wanda ya halarci jana'iza ko makokin Danlami.

Danlami ne mutum na bakwai da ya rasu sakamakon annobar korona a jihar Gombe.

An sallami wasu mutum 125 daga cibiyar killacewa bayan warkewa da suka yi amma mutum 23 na cibiyar.

Ya ce tunda mamacin mamba ne kwamitin yaki da cutar korona na jihar, za a tantance tare da yi wa 'yan kwamitin gwajin cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng