Dakatar da Oshiomhole: Babbar kwanciyar hankali ta samu APC - Jigon APC
Darakta Janar na Voice of Nigeria (VON), Osita Okechukwu, ya bayyana dakatar da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da kotun daukaka kara tayi a matsayin babban kwanciyar hankali ga jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce ya amince zai taimaki takwaransa na jihar Edo, Godwin Obaseki, don koyawa Oshiomhole darasi a jihar.
“Na amince zan taimaki Obaseki don koya wa Oshiomhole darasi a jihar Edo. Oshiomhole ya koma ya tambayi Amechi yadda muka kare,” Wike ya wallafa a shafinsa na Twitter a jiya Talata.
A wata takarda da aka fitar a Abuja, Okechukwu ya ce: “An rabu da kwallon mangwaro, an huta da kuda. Babu shakka Kwamared Adams Oshiomhole bashi da amfani a matsayin shugaban jam’iyyarmu mai albarka.
“An dakatar da shi amma saboda taurin kai ya ki daina ayyukan jam’iyyar don yin biyayya ga kundun tsarin mulkin APC.”
Okechukwu ya ce "duk ta ya mutum da ya rasa gundumarsa, karamar hukuma da jiha zai zama shugaban jam’iyya na kasa?
“Abun farin cikin shine yadda dakatar da shi da aka yi za ta bada damar gyarawa da saita jam’iyyar don tabbatar da nasara.
“A gaskiya dole ne mu kiyaye tare da kara duba yadda Adams ya jagoranci jam’iyyar. Ya samu nasara ko koma baya aka samu a jam’iyyar? Faduwa yayi warwas,” Okechukwu ya kara cewa.
KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar Katsina: 'Yan sanda sun kama shugaban CNG
Idan za ku tuna kotun daukaka kara da ke Abuja ta jaddada dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
A ranar 4 ga watan Maris ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar wasu mambobin APC shida na jihar Edo wajen dakatar da Oshiomhole.
A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa wani sashe na jam'iyyar APC ta bukaci a kori Gwamna Godwin Obaseki da wasu mutum biyu na jam'iyyar sakamakon zargin su da ake da al'amuran zagon kasa ga jam'iyya.
Bangaren ya bukaci kwamitin ayyuka na kasa karkashin jagorancin Oshiomhole da ya sallami Obaseki wanda cikin kwanakin nan aka haramtawa fitowa takara.
Bangaren da ya samu jagorancin Kanal David Imuse ya sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa ba za su amince da ayyukan zagon kasa ga jam'iyyar ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng