Obaseki: Ina goyon bayan Abokina kuma ‘Danuwana ya zarce – Inji Dankwambo
A daidai lokacin da gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya fice daga jam’iyyar APC bayan an hana sa neman tikitin takara, wasu sun fara kira ga Obaseki ya sauya-sheka.
Tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya na cikin wadanda su ke goyon bayan Godwin Obaseki ya zarce a kan kujerarsa ta gwamna a jihar Edo.
Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa tsohon takwaransa Godwin Obaseki ya cancanci ya sake wani wa’adi a matsayin gwamna, saboda irin abubuwan da ya yi.
Dankwambo wanda ya yi mulki a jihar Gombe a karkashin jam’iyyar PDP tsakanin 2011 zuwa 2019, ya kira Obaseki da Aboki kuma Danuwansa.
“Ina goyon bayan Abokina kuma ‘Danuwana, gwamna Godwin Obaseki ya zarce a kan mulki. Wanda ya yi abin kwarai ya cancanci ya maimaita kujera.” Inji Ibrahim Dankwambo.
KU KARANTA: Na kusa fadawa Duniya matakin da zan dauka - Obaseki
Dr. Ibrahim Dankwambo ya bayyana wannan ne a shafinsa na sada zumunta na Twitter na @HEDankwambo a safiyar ranar Litinin 15 ga watan Yuni, 2020.
A jiya Talata da karfe 12:17 na rana, ‘dan siyasar ya sake tofa albarkacin bakinsa a kaikaice game da rikicin da ake zargin an samu tsakanin Adams Oshiomhole da gwamnan na Edo.
“Siyasar uban-gida ta na toshe cigaban tattalin arziki. Ta na kafa tsarin da ke jawo a take talakawa domin a bautawa iyayen gidan siyasa.” Inji Dankwambo.
Tsohon gwamnan na PDP ya kara da cewa: “Dole tsarin shugabancinmu ya ba talakawa karfi domin a karkata sabuwar akalar shugabanci wajen kawo cigaba a kasa da gida.”
A jiya kuma Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana abin da ya tattauna da shugaban kasa a lokacin da su ka sa labule, ya ce an ba shi tabarrukin tazarce a APC.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng