Kudin shan wutar lantarki zai karu a farkon watan Yuli – Saleh Mamman

Kudin shan wutar lantarki zai karu a farkon watan Yuli – Saleh Mamman

- Gwamnatin Tarayya ta ce sabon farashin wutar lantarki zai fara aiki ne a watan Yuli

- A baya an yi ta korafi game da karin kudin a lokacin da ake fama da annoba a Duniya

- Gwamnatin Najeriya ta ce halin da annobar ta jefa kasashe ya taba sha’anin lantarkin

A makon nan ne gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa maganar karin kudin wutar lantarki ya na nan, duk da surutan da kungiyoyi su ka rika yi a game da shirin da ake yi.

A jiya ranar Talata, 16 ga watan Yuni, 2020, Ministan harkokin wutar lantarkin Najeriya, Sale Mamman, ya ce sabon tsarin farashin wutan zai fara aiki a Yuli.

Injiniya Sale Mamman ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan lamarin wutar lantarki a birnin tarayya.

Sale Mamman ya ce gwamnati za ta cigaba da shirin da ta dauko na kara farashin wutan ne domin annobar COVID-19 ta yi tasiri a kan ‘yan kasuwar lantarkin.

Ministan ya shaidawa Sanatocin kasar cewa hukumar NERC ta yi niyyar fara amfani da sabon farashin wutan ne a watan Afrilun 2020, amma sai aka saurara.

KU KARANTA: Ana neman Ministan wuta ya ajiye aiki

Kudin shan wutar lantarki zai karu a farkon watan Yuli – Saleh Mamman
Saleh Mamman
Asali: Facebook

“Hakika, annobar cutar (COVID-19) ta riga ta yi tasiri wajen rage karfin aiki saboda matakan da aka bi a Duniya wajen takaita yaduwar cutar.” Inji Mamman.

"Saboda haka wannan ya taba karfin wutan da ake samu da kuma bukatar lantarki a ko ina.”

“Halin da harkar wuta ta ke a Najeriya shi ne ana kashe makudan kudi wadanda aka dogara da kungiyoyin kasashe masu bada tallafi, da bashi da kuma kudi daga kasafin kasa.”

Ministan kasar ya shaidawa Sanatocin cewa: “A game da ayyukan da mu ka samu kudin da za su dauki nauyinsu, ba mu sa ran a samu wata matsala.”

Yayin da wasu su ke nuna rashin jin dadinsu a game da wannan, Ministan ya ce su na neman hanyar da za abi wajen samun kudi daga waje domin ganin an inganta harkar wutan kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel