Gaidom: Sakataren APC ya soki Jam’iyya a kan ba Ajimobi rikon kwarya

Gaidom: Sakataren APC ya soki Jam’iyya a kan ba Ajimobi rikon kwarya

Bayan kotun kotun daukaka kara ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, an nada Abiola Ajimobi a matsayin shugaban riko.

Sai dai kuma mataimakin sakataren APC, Victor Giadom ya fito ya na sukar wannan matsaya da jam’iyyarsa ta dauka inda ya nuna cewa shi ne ya dace ya dare kan kujerar shugaban jam’iyyar.

Magoya bayan Cif Victor Giadom a tafiyar jam’iyyar APC sun fara nuna adawarsu ga Abiola Ajimobi. Wadanda ke tare da Giadom sun bayyana haka ne a wani jawabi da su ka fitar a jiya.

Lauyan jigon jam’iyyar, Wole Afolabi ya sanar da jaridar Vanguard cewa shari’ar da babban kotun tarayya ta yi a watan Maris ya ruguza duk wasu matakai da Adams Oshiomhole ya dauka a ofis.

Daga cikin abubuwan da Oshiomhole ya yi bayan dakatar da shi a watan Maris akwai nada Abiola Ajimobi a matsayin mataimakin shugaban APC, Lauyan ya ce wannan nadi bai da wuri a doka.

Afolabi ya ce: “Hankalinmu ya zo ga wata sanarwa da ta fito daga bakin sakataren yada labaran APC na cewa Sanata Abiola Ajimobi zai zama mukaddashin shugaban APC bayan dakatar da Adams Oshiomhole daga ofis da kotun daukaka kara ta yi.”

KU KARANTA: Abiola Ajimobi zai rike kujerar Adams Oshiomhole

Gaidom: Sakataren APC ya soki Jam’iyya a kan ba Ajimobi rikon kwarya
Shugabannin Jam'iyyar APC
Asali: Twitter

“Mu na so mu sanar da cewa an fitar da wannan bayani ne tare da jahiltar hukuncin da babban kotun tarayya ta yi a ranar 16 ga watan Maris ta bakin Alkali mai shari’a SU Bature a kara mai lamba ta FCT/HC/M/6447/2020, inda aka ce Victor Giadom ne zai zama shugaban jam’iyya saboda dakatarwar Adams Oshiomhole.”

“An zartar da wannan hukunci ne a ranar da kotun daukaka kara ta ceci Adams Oshiomhole na wani dan lokaci. Yanzu da kotun ta tabbatar da wannan dakatarwa, zai yi daidai ace an tabbatar da hukuncin Victor Giadom.”

A dalilin haka ne Lauyan ya bayyana cewa sun rubutawa jami’an tsaro takarda cewa a kama duk wani wanda ya yi kokarin shiga ofis da sunan shi ne shugaban jam’iyya face Victor Giadom.

A makon nan, Legit.ng Hausa ta fitar da rahoto cewa Abiola Ajimobi ya na jinyar cutar COVID-19 a wani asibiti da ke Legas. Yanzu mako biyu kenan tsohon gwamnan ya na asibiti bai warke ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel