Rochas Okorocha ya fada mani in yi wa EFCC karya – Shugaban kamfanin Zigreat

Rochas Okorocha ya fada mani in yi wa EFCC karya – Shugaban kamfanin Zigreat

Binciken da ake yi game da kwangilolin da Rochas Okorocha ya bada a lokacin ya na gwamnan jihar Imo ya canza salo bayan da shugaban wani kamfani ya bayyana domin ya bada shaida.

Shugaban kamfanin Zigreat International, Stanley Enwereaku ya bayyana cewa Rochas Okorocha ne ya yi sanadiyyar da ta sa ya yi wa hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin Najeriya zagon-kasa karya.

Mista Stanley Enwereaku ya bayyana wannan ne a lokacin da ya bayyana, ya na bada shaida a gaban hukuma.

“Lokacin da hukumar EFCC ta gayyaci kamfani na zuwa ofishinsu da ke garin Enugu, tsohon gwamna Rochas Okorocha ya roke ni in fadawa EFCC cewa kamfanin Zigreat ya yi duk ayyukan da aka ambata da sunansa.”

Enwereaku ya fadawa masu binciken cewa ya yi wannan karya domin ya kare Sanata Rochas Okorocha. Shugaban kamfanin ya ce tsohon gwamnan ya gode masa bayan ya dawo saboda kare gwamnatinsa da ya yi.

KU KARANTA: Ka da a hana Almajiranci - Okorocha

Rochas Okorocha ya fada mani in yi wa EFCC karya – Shugaban kamfanin Zigreat
Rochas Okorocha
Asali: Twitter

“Lokacin da na dawo daga Enugu, gwamnan ya gode mani na aikin kwaran da na yi. Ya kuma umarce ni in koyawa sauran ‘yan kwangila yadda za su yi wa EFCC karyayyaki.” Inji Enwereaku.

Shugaban kamfanin na Zigreat ya koka game da yadda jami’an hukumar tara haraji watau FIRS su ka taso shi a gaba a kan wasu Naira miliyan 100 da su ka shiga hannun kamfaninsa.

Mista Enwereaku ya ce bai ci wadannan miliyoyi ba, iyaka kurum an yi amfani da shi ne wurin raba kudin. Enwereaku ya ce ya yarda ya yi abin da bai dace ba, amma umarnin Okorocha ya ke bi.

“Ina shirin in koma wajen EFCC in wanke kai na daga karyar da na yi masu. Abin da na ke fada ya sha ban-ban da abin da na fadawa EFCC. Ina tsoron abin da za su yi mani, amma duk da haka, zan je in fada masu gaskiya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel