Kwamitin Osinbajo ya kawo maganar dakatar da zuwa sansanin hidimar kasa

Kwamitin Osinbajo ya kawo maganar dakatar da zuwa sansanin hidimar kasa

Kwamitin tattalin arziki na ESC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ke jagoranta ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin shiga sansani da masu yi wa kasa hidima su ke yi.

Farfesa Yemi Osinbajo da kwamitin na sa sun bada shawarar a tsaida wannan al’ada ta zuwa sansanin NYSC inda ake horas da matasan da za su yi bautar kasa.

A rahoton da kwamitin mataimakin shugaban kasar ya mikawa gwamnatin tarayya, ta tsaida matsaya cewa nan da watanni 24, ka da a ajiye mutane a sansanonin hukumar NYSC.

“Matakin gaggawan da za a dauka a harkar ilmi zai taimaka wajen yaki da annobar cutar COVID-19 tare da tabbatar da cewa ana bada tazara a wajen daukar karatu.” Inji kwamitin.

Kwamitin ya kuma bukaci a rika amfani da kafofin zamani wajen daukar karatu. “Za ayi amfani da kafafen yanar gizo ko kuma yada labarai wajen bada darasi.”

KU KARANTA: Mutanen Katsina sun jefawa fadar Shugaban kasa kalubale

Kwamitin Osinbajo ya kawo maganar dakatar da zuwa sansanin hidimar kasa
Yemi Osinbajo Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: Twitter

Daga cikin shawarwarin da kwamitin ESC ya bada shi ne: “A rika yin bikin yaye wadanda su ka kammala hidimar kasa ba tare da an samu taruwar jama’a ba.”

“A irin haka kuma, a fara la’akari da dakatar da shiga sansanin horas da masu bautar kasa da ake yi da akalla watanni 24, tare da bada damar a aika masu bautar kasa zuwa wuraren da za su yi aiki.”

“Wannan zai taimaka wajen ganin ba a samu matasa jibge da su ke jiran su tafi NYSC ba.”

A watan Maris ne aka rufe sansanonin NYSC bayan barkewar cutar COVID-19 a Najeriya. A makon jiya NYSC ta fara maganar dawowa bakin aiki, sai kuma ga rahoton wannan kwamiti.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel