Annobar COVID-19: Abiola Ajimobi bai samu sauki ba har yanzu

Annobar COVID-19: Abiola Ajimobi bai samu sauki ba har yanzu

- Tsohon Gwamna Abiola Ajimobi ya na fama da Coronavirus har yanzu

- An fara damuwa da halin da Ajimobi mai shekara 70 ya ke ciki a asibiti

- Sanata Ajimobi ya na jinya ne a asibitin da Sanatan Legas ya mutu jiya

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya na cigaba da zaman jinya a asibitin First Cardiologist and Cardiovascular Consultants da ke Legas inda ya ke fama da cutar Coronavirus.

Jaridar Punch ta ce makonni biyu kenan har yanzu ba a sallami ‘dan siyasar daga asibiti ba. Mai dakin tsohon gwamnan, Florence Ajimobi ta samu lafiya, kuma ta bar asibiti har ta koma gida.

Abiola Ajimobi wanda shi ne sabon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudancin Najeriya ya na asibiti ne tun ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020.

Rahotanni sun bayyana cewa Abiola Ajimobi ya fara jinya ne a gida kafin cutar ta buge shi har ya zo asibiti. An tabbatar da cewa tsohon gwamnan ya na dauke da cutar ne bayan an yi masa gwaji.

KU KARANTA: Wani tsohon Farfesa ya mutu a Najeriya

Annobar COVID-19: Abiola Ajimobi bai samu sauki ba har yanzu
Abiola Ajimobi
Asali: Depositphotos

Wani na-kusa da Sanata Ajimobi ya ce tsohon gwamnan ya na fama da wata rashin lafiya wanda ba ta rasa alaka da yawan shekarunsa. Ajimobi ya cika shekara 70 da haihuwa ne a karshen 2019.

“Tsohon gwamnan ya na asibiti na tsawon makonni biyu kuma har yanzu babu wani sauki da ake samu a jikinsa. Sai dai mu na fatan abubuwa su yi kyau.” Inji wannan wanda ke da kusancin da shi.

Ya kara da cewa: “Abin mamakin shi ne wanda Ajimobi ya dauki cutar daga wurinsa ya warke, an sallame sa.”

“(Abiola Ajimobi) tsohon gwamnan ya na da wata cuta wanda ta ke kawo masa nawa wajen samun lafiya. Mu na fatan ya warke kwanan nan.” Inji sa.

A jiya ne kuma mu ka ji cewa Sanatan Legas, Adebayo Osinowo ya rasu inda ake zargin ya yi fama ne da COVID-19. Sanatan ya cika ne a wannan asibiti da Ajimobi ya ke kwance a yanzu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel