Kwamishinan ‘Yan Sanda ya sa ganima ga wanda ya nemo Adamu Yankuzo

Kwamishinan ‘Yan Sanda ya sa ganima ga wanda ya nemo Adamu Yankuzo

Dakarun ‘yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da cewa sun yi nasarar cafke mutane 50 da ake zargin su na da hannu a kashe-kashen da ake yi a kananan hukumomi akalla takwas na jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda na Katsina, CP Sanusi Buba ya bayyana wannan a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida. Sanusi Buba ya ce jami’ansa sun yi ram da miyagun da ke kashe Bayin Allah.

Da ya ke bada wannan sanarwa, kwamishinan ya kuma bayyana cewa su na neman wani Mutumi mai suna Adamu Alieru Yankuzo, har kuma ya sa kudi a kan duk wanda ya iya gano masu shi.

Adamu Alieru Yankuzo mutum ne mai shekaru 45 da haihuwa, kuma ya fito ne daga kauyensu da ake kira Yankuzo, a cikin karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Duk wanda ya taimakawa ‘yan sanda da inda wannan mutumi ya ke, ko kuma ya yi sanadiyyar hanyar da za su cafke shi, zai samu kyautar Naira miliyan biyar.

A halin yanzu jami’an tsaro su na neman wannan watau Adamu Alieru Yankuzo ko kuma gawarsa. Kawo yanzu babu wanda ya fito ya bayyana wata masaniya.

KU KARANTA: Gwamna Masari ya bada gari, ya ce ya gaza kare rayukan al'umma

Kwamishinan ‘Yan Sanda ya sa ganima ga wanda ya nemo Adamu Yankuzo
Gwamnan Jihar Katsina
Asali: UGC

Daga cikin kokarin da jami’an ‘yan sandan su ka yi, sun kama mutane da-dama da ake zarginsu ne su ke garkuwa da jama’a, da fashi da makami da kuma satar dabbobi a garuruwan Katsina.

Makaman da aka kama a hannunsu kuwa sun hada da bindigogin AK-47 10, kananan bindigogi 5 da harba-ka-labe 25. An kuma samu motoci 5, babura 20 duk a hannun wadannan miyagun.

Sanusi Buba ya kuma tabbatar da cewa ‘yan sanda sun yi ram da wadanda su ka shiga kauyen Kadisau a karamar hukumar Faskari. Ana zargin wadannan ‘yan bindiga sun hallaka mutum 50.

Wadanda su ka shiga hannun jami’an tsaro sun hada da Bello Usman, daga Dutsinma, Usman Sule daga Faskari, Surajo Yusuf daga Sabuwa, wadanda duk matasa ne a cikin jihar Katsina.

Usman Bello ne ya tonawa Adamu Aliero Yankuzo asiri inda ya bayyana cewa Yankuzo ne ya kai hari a Yantumaki domin huce takaicin ‘dansa Sulaiman Adamu Aleiru da hukuma ta kama.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel