Ganduje: Sauye-sauyen da aka kawo ya jawo tsohon Sarki Sanusi II ya rasa rawaninsa

Ganduje: Sauye-sauyen da aka kawo ya jawo tsohon Sarki Sanusi II ya rasa rawaninsa

A Ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, 2020, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana game da tsohon sarki Muhammadu Sanusi II wanda ya tsigewa rawani a watan Maris.

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa sam bai yi nadamar kawo gyare-gyaren da su ka yi sanadiyyar tsigewa Muhammadu Sanusi rawani a matsayin sarkin Kano ba.

Tsohon gwamnan babban bankin kasar ya bar karagar mulki ne bayan gwamnatin Kano ta tsige shi, sannan kuma da farko jami’an tsaro su ka yi gaba da shi zuwa wani kauye a jihar Nasarawa.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana ne domin yin bikin damukaradiyya ta kasa, inda ya ambaci kafa sababbin masarautun da ya yi a matsayin daya daga cikin nasororin gwamnatinsa.

Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa sababbin masarautun da ya kafa a kasar Bichi, Rano, Gaya da kuma Karaye sun taimakawa rayuwa da cigaban mutanen yankin da daukacin jihar Kano.

KU KARANTA: Dattawan Kano sun kai Ganduje kotu kan sauke Sarki Sanusi

Sauye-sauyen da aka kawo ya jawo tsohon Sarki Sanusi II ya rasa rawaninsa
Abdullahi Ganduje Hoto: Twitter
Asali: Twitter

A cewar gwamnan, Malam Muhammadu Sanusi II ya rasa matsayinsa na Sarki ne bayan da ya gaza amincewa da tsare-tsaren da gwamnatin Kano ta kawo domin cigaban al’ummar jihar.

Ganduje ya kuma nuna cewa babu ranar taba wadannan masarautu da aka kirkira a shekarar 2019.

Tsohon sarkin Kano wanda ya ki yin na’am da sauye-sauyen da aka yi, dole ya bar gadon mulki domin a kawo gyara, kuma wadannan masarautun su na nan din-din-din.” inji gwamnan.

Mai girma gwamnan ya yarda cewa karar da aka rika kai gwamnati a kotu ya na cikin abubuwan da su ka jawo aka samu bacin lokaci wajen kammala gyare-gyaren da aka yi wa masarautu.

Dr. Ganduje ya zargi Muhammadu Sanusi II da wasu dattawan jihar Kano wadanda su ke goyon bayan tsohon sarkin da hannu wajen maka gwamnatinsa a kotu domin ganin an taka masa burki.

“Amma yau babu wata shari’a a game da masarautun a gaban kotu.” Inji gwamna Ganduje.

Jaridar Punch ta ce gwamnan ya yi magana game da binciken badakalar filin da aka yi a lokacin Muhammadu Sanusi II, inda ya ce hukuma za ta cigaba da bincike yadda doka ta tanada.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel